Babu Maganar Komawa Majalisa Bayan Ministar Tinubu Ta Fado ta Kai a Kotun Zabe
- Murnar jam’iyyar APC ya koma ciki tun da Alkalai su ka tabbatar da nasarar LP a zaben ‘dan majalisar Isikwuato/Umunneochi
- A yayin da Lauyoyin Hon. Nkeiruka Onyejeocha su ka kunyata a kotun daukaka kara, Cyriacus Sunday Umeha ya samu nasara
- Amma kotu ta ce a sake yin zabe nan da watanni uku, bayan Denis Agbo ya fara sabawa da zaman majalisar wakilan tarayya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Kotun daukaka kara da ke zama a garin Legas ta yi waje da hukuncin kotun korafin zaben ‘dan majalisar Isikwuato/Umunneochi.
Kamar yadda Premium Times ta kawo rahoto a ranar Asabar, hukuncin ya na nufin Hon. Amobi Ogah zai cigaba da rike kujerarsa a majalisa.
LP ta doke Minista a kotu
Hon. Nkeiruka Onyejeocha wanda yanzu haka Minista ce a gwamnatin Bola Tinubu ta yi rashin sa’a wajen komawa majalisar wakilan tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta gamsu LP ta na da kuri’u 11,769 yayin da APC ta samu 8,752 a zaben ‘dan majalisa mai wakiltar Isiukwuato/Umunneochi a Abia.
Hon. Matthew Nwogu ya yi galaba a LP
Sannan Ali Babandi Gumel ya jagoranci hukucin kotun daukaka karar, ya sake ba LP nasara a zaben ‘dan majalisar Aboh Mbaise/Ngor Okpala.
Alkalin babban kotun ya ce Hon. Matthew Nwogu mai wakiltar Aboh Mbaise/Ngor Okpala ta jihar Abia ne halataccen wanda ya lashe zaben 2023.
Leadership ta ce Hukuncin Gumel ya kawo karshen kalubalantar zaben a APC ta ke yi a kotu.
Kotu: "LP ta ci zaben zaben Ezeagu/Udi"
Idan aka koma jihar Enugu, jam’iyyar adawa ta LP ta kuma yin nasara a kotun karshe da ake sauraron karar majalisar tarayya a tsarin mulkin kasa.
Daily Post ta ce Alkalan da su ka saurari karar zaben Ezeagu/Udi a kotun daukaka kara na Legas sun tabbatar da nasarar Cyriacus Sunday Umeha.
Sai dai duk da murnar da magoya bayan LP su ke yi, Denis Agbo ya na fuskantar barazana bayan babban kotu ta tsige shi, ta ce a sake sabon zabe.
Jaridar ce kotun daukaka kara ta gamsu da korafin Dr Oby Ajih na cewa rashin tambarin APC a takardun zabe ya saba ka’ida, sai an sake takara.
Shari'ar zabe a kalubalen NNPP a kotu
Ku na da labari shari’ar zabensa da Nasiru Yusuf Gawuna ya na cikin wadanda Abba Kabir Yusuf ya ji kunya a kotu bayan hawansa kan mulki a Mayu.
Sauran shari’o’i da aka yi galaba a kan Gwamnan sun hada da na rusa shagunan al’umma da sabaninsa da magabacinsa, Abdullahi Ganduje.
Asali: Legit.ng