Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na Labour Party a Abia

Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na Labour Party a Abia

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen NASS mai zama a Umuahia, jihar Abia ta rushe nasarar ɗan majalisar tarayya na jam'iyyar Labour Party
  • Yayin yanke hukunci ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, Kotu ta maye gurbin ɗan majalisar da 'yar takarar jam'iyyar APC, Honorabul Nkeiruka Onyejeocha
  • Ta umarci hukumar zaɓe INEC ta janye shaidar lashe zaɓen da ta baiwa Ogah, ta bai wa halastacciyar 'yar majalisa

Abia state - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben 'yan majalisar tarayya mai zama a Umuahia, babban birnin jihar Abiya ta yanke hukunci kan zaben mazaɓar Isuikwuato/Umunneochi.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Kotun ta tsige mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Isuikwuato/Umunneochi, Honorabul Amobi Ogah a inuwar jam'iyyar Labour Party.

Kotu ta sauke Ogah, ta baiwa yar takarar APC nasara a Abia.
Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na Labour Party a Abia Hoto: Amobi Ogah, Nkeiruka Onyejeocha
Asali: Facebook

Bayan nan ne Kotun ta umarci hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta kwace takardar shaidar lashe zaɓe daga hannun Honorabul Ogah, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam’iyyar Labour Ta Ki Amincewa Da Hukuncin Kotun Ƙararrakin Zabe, Ta Fadi Mataki Na Gaba

Haka zalika ta umarci INEC ta bai wa wanda ta shigar ƙara kuma 'yar takara a inuwar jam'iyyar APC, Honorabul Nkeiruka Onyejeocha, takardar shaida zama wacce ta lashe zaɓe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan hukunci da Kotu ta yanke na nufin kwace kujerar majalisar tarayya daga hannun Ogah na LP tare da ayyana 'yar takarar APC a matsayin wacce ta ci zaɓe.

Daga nan Ƙotun ta tabbatar da nasarar Onyejeocha, inda ta ayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaɓen mamban majalisar tarayya ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar Peter Obi

Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben shugaban ƙasa ta yi fatali da ƙarar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party ya ƙalubalanci nasarar shugaba Tinubu.

Kwamitin alkalan Kotun karkashin mai shari'a Haruna Tsammani ya bayyana cewa ƙarar Peter Obi da jam'iyyar LP ba ta cancanta ba, bisa haka ya yi watsi da ita.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Babban Sanatan Jam'iyyar APC, Ta Bayyana Dalilanta

Kotun Zabe Ta Tsige Sanatan Delta Ta Kudu, Ta Yi Umurnin Sake Zabe Cikin Kwana 90

A wani labarin na daban kuma Kotun sauraron korafe-korafen zaben 'yan majalisar tarayya a Delta ta tsige sanatan APC na Delta ta kudu daga kujerarsa.

Da take yanke hukunci a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, kotun ta ba da umurnin janye takardar shaidar cin zaben Sanata Thomas Onowakpo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel