Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi T. B Joshua

Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi T. B Joshua

- Malamin majami'ar dukkan ƙasashe, T. B Joshua ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 57 a duniya

- An haifi Joshua ne a ranar 12 ga watan Yuni 1963, ya rasu gab da zagayowar ranar haihuwarsa

- Marigajin ya taba amsar lambar girmamawa ta ƙasa a shekarar 2008, yayin da Amurka ta turo mishi da saƙon yabo na musamman

Wanda ya ƙirƙiro majami'ar dukkan ƙasashe, Fasto Temitope Balogun Joshua, da aka fi sani da T. B Joshua ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 57, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Kare Kansa, Ya Bayyana Dalilin Gwamnatinsa Na Dakatar da Twitter a Najeriya

An fara raɗe-raɗin mutuwar fitaccen malamin majami'ar da sanyin safiyar Lahadi, amma daga baya majami'ar ta tabbatar, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa 7 game da marigayi T. B Joshua.

Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi T. B Joshua
Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi T. B Joshua Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

1. An haifi T. B Joshua a ranar 12 ga watan Yuni, 1963. Ya rasu yana da shekara 57 gab da zagayowar ranar haihuwarsa.

2. A 2009, Joshua ya ƙirƙiri ƙungiyar ƙwallon ƙafa 'My people FC' biyu daga cikin yan tawagar ƙungiyar, Sani Emmanuel da Ogenyi Onazi sun shiga tawagar Najeriya a 2009 da ta halarci kofin duniya na matasa yan ƙasa da shekara 17.

Emmauel ya samu damar ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar SSC Lazio ta ƙasar Italiya yayin da Onazi ya zama ɗan wasa mai muhimmanci a babbar tawagar Najeriya 'Super Eagles.'

3. Bayan girgizar ƙasa da akayi a Haiti 2010, Joshua ya aike da tawagar likitoci da masu bada agaji ga yankunan da abun ya shafa, har ya gina wani asibitin sarari ‘Clinique Emmanuel’.

KARANTA ANAN: NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i

4. Fitaccen malamin majami'an ya tura agajin sa ga ƙasashe kamar India, Philippines, da Ghana lokacin da suka fuskanci wata matsala.

5. Ya gina makaranta sannan ya tafiyar da ita a Lahore, Pakistan, mai suna 'Emmanuel School'. Ya kuma gyara wata makaranta a Ecuador wanda girgizar ƙasa ta lalata.

6. An baiwa T. B Joshua lambar girmamawa ta ƙasa a shekarar 2008, yayin da ƙasar Amurka ta turo masa da sakon yabo na musamman.

7. Gwamnatin Kamaru ta saka sunansa a cikin jerin sunayen waɗanda bata amince da su ba 'Blacklist' Shekarar 2010.

A wani labarin kuma Kamfanonin Sadarwa MTN, Airtel, Glo Sun Rufe Damar Shiga Twittter a Najeriya

Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun rufe damar hawa dandalin sada zumunta na twitter a faɗin ƙasar.

Kamfanonin da suka haɗa da MTN, Glo, Airtel, 9mobile da sauransu, sun yi haka ne bisa umarnin NCC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel