Rarara: Farfesa Ya Yi Tonon Silili, Ya Fallasa Masu Daukar Nauyin Wakokin 'Cin Mutunci'

Rarara: Farfesa Ya Yi Tonon Silili, Ya Fallasa Masu Daukar Nauyin Wakokin 'Cin Mutunci'

  • Abdalla Uba Adamu ya na ganin nan gaba za a ji Dauda Kahutu watau Rarara ya na zagin Bola Ahmed Tinubu a wakokinsa
  • Farfesan ya ce babu wasu abubuwan ilmantarwa a wakokin Rarara, ya zarge shi da yin zambo domin bata sunan ‘yan siyasa
  • Uba Adamu ya ce kafin ya taba Muhammadu Buhari, marokin ya juyawa Ibrahim Shekarau da Rabiu Musa Kwankwaso baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Abdalla Uba Adamu Farfesa ne a fannoni biyu na ilmi, daga ciki akwai harkar sadarwa da ya yi fice a jami’ar Bayero da ke Kano.

A wata hira da ya yi da rediyon Freedom, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya yi magana a a kan babatun da aka ji Dauda Kahutu Rarara ya na yi.

Masanin ya nuna cewa kamar yadda mawakin ya ke sukar Muhammadu Buhari a yau, haka gobe zai koma zagin shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu zai canja shugaban ma'aikatan fadarsa, Gbajabiamila? Shugaban Kasa ya magantu

Rarara da Bola Tinubu
Dauda Rarara da Bola Tinubu Hoto: @Aminugarbadogo1
Asali: Twitter

Abdalla Uba Adamu ya na zargin cewa kudi ake ba Rarara domin ya wanke mutum ko ya bata masa suna a cikin wakokinsa da yake rerawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya kara da cewa wakokin Dauda Kahutu da aka fi sani da Rarara ba su dauke da ilmantarwa ko wayar da kai sosai sai tarin zambo.

'Yan Kano su ke daukar nauyin Rarara

Abin takaicin a cewar Farfesa Uba Adamu shi ne, wasu mutanen Kano ne su ke bada kudi saboda mawakin ya ci mutuncin ‘yan siyasa a wakarsa.

Alal misali, a wakar 'Tinubu ya kada tsula', Farfesan ya ce an fadi wanda ya dauki nauyin wakar, ya ce haka ya nuna kazantar siyasar Kano.

Akasin yadda ake tunani, Uba Adamu ya ce ba yanzu Rarara ya fara sukar Buhari ba, tun ya na gwamnati ya soke shi a wata waka kan tsaro.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya hango abin da zai faru idan Majalisa ta tsige Gwamnan Ribas

'Rarara zai yi wa Tinubu haka'

Wannan halinsa ne, na duba wakokinsa kusan 82, kusan duk abin da yake fada a cikin wakokinsa, ya na zagin wanda da uban gidansa ne.
Shi kadai ne a cikin mawaka yake da wannan salon, tun daga kan (Ibrahim) Shekarau ya fara har zuwa kan (Rabiu Musa) Kwankwaso.
Kuma ina fada maka, tabbas sai ya yi wa Abdullahi T. Gwarzo da kuma Bola Ahmed Tinubu. - Farfesa Abdallah Uba Adamu

Rarara ya na da magabata a mawakan Duniya

Da yake ya na nazarin wakoki, Farfesan ya ce mawakan duniya da na gida irinsu Shata da Dankwairo su kan ci mutuncin wasu a wakokinsu.

Magabatan fitaccen mawakin sun yi wake-wake su na cin mutuncin manya kamar su Aminu Kano, abin da ya ce ba a saba ji a kasashen waje ba.

Mawaki Rarara ya na neman mukamai

Ana da labari Dauda Rarara ya ce kyau idan za a kafa gwamnati, ya kawo sunayen Ministoci ko da biyu ne domin ya san wadanda su ka wahala.

Kara karanta wannan

Sirrin Kasuwancin da Mahaifinmu Ya Fada Mani Kafin Ya Bar Duniya – Aminu Dantata

A taron ‘yan jarida da ya kira, Alhaji Rarara ya ce Aminu Masari da Abdullahi Ganduje rak ne a gabansa wajen tallata takarar Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel