Tinubu Zai Canja Shugaban Ma'aikatan Fadarsa, Gbajabiamila? Shugaban Kasa Ya Magantu
- Shugaba Tinubu ya yi martani kan korafe-korafen da ake yi kan shugaban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila
- Tinubu ya ce ya amince da gaskiyar Femi dari bisa dari kuma ya na da kwarin gwiwa a kansa wurin gudanar da ayyuka
- Shugaban ya bayyana haka ne a yau Litinin 30 ga watan Oktoba a Abuja yayin gudanar da taron majalisar zartarwa a Abuja
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matsayarsa kan cece-kuce da ake kan shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila.
Tinubu ya bayyana haka ne a yau Litinin 30 ga watan Oktoba inda ya ce ya amince da gaskiyar Femi dari bisa dari kuma ya na da kwarin gwiwa a kansa.
Wane zargi ake yi wa Femi da Tinubu ya yi martani?
Ana zargin cewa Femi na siyar da wasu nade-naden gwamnati inda ake tunani Tinubu ka iya sauya shi a mukamin nasa, Legit ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan wata majiya na zargin Gbajabiamila da sauya duk wata sa hannu da Tinubu ya yi zuwa wani abu daban.
Tinubu ya bukaci dukkan ma su wannan kare-rayi da korafe-korafe da su dakatar da su haka nan kuma daga wannan lokaci ba ya son sake jin su.
Hausa Legit ta ji ta bakin wasu kan wannan mataki na Tinubu:
Adamu Anas ya ce ai daman dan uwanshi ne, ba wani mataki da zai dauka a kanshi ba kaman Hausawa ba.
Aishatu Muhammad ta ce:
"Ai daman su, su na kishin 'yan uwansu ko da kuwa babban laifi su ka aikata, zai yi wahala kaga hakan ta faru."
Sadiq Abubakar ya ce tun da an tabbatar ya na karbar na goro, ya kamata Tinubu ya dauki mataki a kansa.
Rikici ta barke tsakanin sanatoci da mambobin majalisar wakilai
A wani labarin, mun samu rahoton cewa rikice ta barke tsakanin majalisun Tarayya guda biyu ka nadin shugabannin hukumar NDDC.
Wannan na zuwa ne bayan majalisar wakilai ta Tarayya ta dakatar da nadin da takwararta da Dattawa ta yi.
Asali: Legit.ng