Sanatoci da ‘Yan Majalisar Tarayya Ana Rikici Kan Nadin Mukamai a NDDC

Sanatoci da ‘Yan Majalisar Tarayya Ana Rikici Kan Nadin Mukamai a NDDC

  • Majalisar dattawa ta tantance wadanda Bola Ahmad Tinubu ya bada sunansu domin su rike hukumar NDDC
  • ‘Yan majalisar wakilai sun ce ba za su yarda a nada su ba domin ba a tuntube su a lokacin aikin tantacewar ba
  • Dokar NDDC ta ce dole ne Sanatoci su hada-kai da majalisar tarayya kafin a rantsar da shugabannin NDDC

Abuja - Majalisar dattawa da ta wakilan tarayya sun samu sabani a kan tantance shugabannin da za su kula da harkokin hukumar NDDC.

Rahoton da aka samu daga Leadership ya ce ‘yan majalisar na fada ne dalilin sunayen da Bola Tinubu ya fitar na jami’an da za su rike hukumar.

Majalisar wakilan tarayya ta dakatar da nadin shugabannin da Sanatoci su ka tantance.

Majalisa
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

NDDC: An tantance Ogboku da Ibie

Kara karanta wannan

Abokai 5 Sun Mutu Tare a Mummunan Hadari a Hanyar Zuwa Daurin Aure

Kwanakin baya majalisar dattawa ta tabbatar da Sam Ogboku da Chiedu Ibie a matsayin shugabannin NDDC, kuma an sanar da shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana jiran shugaban kasa ya ba Ministan Neja-Delta, Abubakar Momoh damar rantsar da shugabannin ne sai aka ji majalisar tarayya ta kawo tangarda.

Gbajabiamila ya taimakawa 'yan majalisa

Jaridar ta ce ana zargin ‘yan majalisar wakilai sun hada-kai da Femi Gbajabiamila, su ka hana a rantsar da shugabannin da Sanatoci su ka tantance.

Dokar kasa ta ce kafin a kai ga nada shugabannin a ofis, sai sun samu amincewar majalisar dattawa tare da tuntubar ‘yan majalisar wakilan kasar.

A kan wannan gaba ne majalisar wakilan tarayya ta huro wuta cewa ba a tuntube ta ba aka fara shirin nada mukaman, abin da ya saba dokar NDDC.

Sanatocin sun yi hujja da Erhiatake Ibori-Suenu

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

Majiya a majalisar dattawa ta musanya zargin, ta ce da sa hannun majalisar wakilai aka yi aikin domin an gayyato Honarabul Erhiatake Ibori-Suenu.

Hon. Ibori-Suenu ita ce shugabar kwamitin harkokin NDDC a karamar majalisar tarayyar. Sahara Reporters ta tabbatar da an samu sabanin nan.

Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi Jr., ya tabbatar da sabani ya shiga tsakaninsu da Sanatoci, yake cewa an sabawa doka.

Rikicin cikin gida a jam'iyyar APC

An samu rahoto cewa jagoran APC na reshen Ribas, Chukwudi Dimkpa ya fadawa Dr Abdullahi Ganduje cewa bai cikin masu cin-amanar jam'iyya.

A wani jawabi da ya fitar, Dimkpa ya gargadi Tony Okocha, ya na mai fada masa ya guji kawo rabuwar kai da sunan tona asirin 'yan zagon-kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel