Hukuncin Kotun koli: A Karshe Tinubu Ya Maida Martani Ga Kalaman Atiku Abubakar

Hukuncin Kotun koli: A Karshe Tinubu Ya Maida Martani Ga Kalaman Atiku Abubakar

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi martani ga Atiku Abubakar, dan takarar PDP a zaben 2023, kan furucinsa game da hukuncin kotun koli
  • A taron manema labarai a ranar Litinin, Atiku ya soki hukuncin babban kotun da ta yi fatali da karar da ya daukaka kan Tinubu, yana mai zarginta da halasta haram a hukuncinta
  • Sai dai Tinubu ya ce Atiku yana murde ra'ayin jama'a ne yayin da yake zargin bangaren shari'a kan kayen da ya sha a zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullun

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi martani ga taron manema labarai na Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, cewa a karshe tsohon mataimakin shugaban kasar ya gano muryarsa.

Kara karanta wannan

Atiku: Kotun koli ta halasta haram da kirkirar takardar bogi

Tinubu ya ce Atiku ya karyata shi a inda ya yi tunanin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar zai nuna dattako ta hanyar sako Najeriya a gaba, amma sai aka samu akasin haka a taron manema labaran.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan labarai da dabaru ya aikewa Legit Hausa a ranar Litinin 30 ga watan Oktoba.

Tinubu ya caccaki Atiku kan taronsa na manema labarai
Tinubu yi martani ga Atiku Abubakar kan hukuncin kotun koli Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya yi jawabi ga yan Najeriya a ranar Litinin karo na farko tun bayan da kotun koli ta yi fatali da karar da ya daukaka kan shugaban kasa Tinibu a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, da kuma tabbatar da nasarar APC a zaben shugaban kasar na 2023.

Atiku ya zargi kotun koli da halasta haram

A taron manema labaran, Atiku ya bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke ya tabbatar da cewa ta na goyon bayan rashin bin doka da almundahana da kuma aikata haram.

Kara karanta wannan

Babu inda zan tafi, Atiku ya magantu kan mataki na gaba bayan hukuncin kotun koli

Amma wani bangare na jawabin Tinubu na cewa:

"Babu kunya shi (Atiku) ya mayar da kansa mai mulkin kama karya ta hanya da salon da ya nemi ruguzawa tare da haramta dukkan hukumomin kasar, duk a kokarin son cimma abin da ya kasa samu ta hanyar zabe."

Shugaban kasar ya kuma zargi dan takarar na PDP da murde ra'ayin jama'a da kuma ganin laifin bangaren shari'a kan kayen da ya sha a zaben.

Najeriya ce ta yi asara, Atiku

A baya mun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ce Najeriya a matsayin ƙasa ta lalace.

Wannan dai na zuwa ne kimanin sa'o'i 72 bayan da kotun ƙoli ta yi watsi da ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya shigar saboda rashin cancanta, tare da tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa na watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng