Hadimin Buhari Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru Idan Majalisa Ta Tsige Gwamnan Ribas
- Tolu Ogunlesi ya nemi sanin laifin da ake tuhumar Simi Fubara da aikatawa da har ‘yan majalisa ke shirin sauke shi daga mulki
- Idan babu laifin da ya aikata, tsohon hadimin shugaban kasar ya ce babu wanda ya isa ya tunbuke Gwamnan jihar Ribas
- Wani tsohon ‘dan majalisa ya ba Gwamna Simi Fubara shawarar ya nemawa kan sa mafitar siyasa kafin lokaci ya kure masa
M. Malumfashi ya yi shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Rivers - Jama’a su na cigaba da tofa albarkacin bakinsu a game da abubuwan da ke faruwa a majlisar dokokin jihar Ribas.
Rahotanni da yawa sun nuna ‘yan majalisar Ribas su na shirin tsige Gwamna Simi Fubara wanda bai wuce watanni biyar a ofis ba.
Tolu Ogunlesi wanda ya taba zama Mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari, ya yi gajeren tsokaci a game da rikicin siyasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifin me Gwamnan Ribas ya aikata?
A bayanan da ya yi a Twitter, Ogunlesi ya nuna cewa ya kamata a fito a fadi laifin da Fubara ya aikata da ya dace a tsige shi a doka.
Idan kuwa aka tunbuke shi ba tare da bin ka’ida ba, tsohon hadimin shugaban Najeriyan ya ce zai koma kujerarsa idan ya je kotu.
Hakan ya na zuwa ne bayan wuta ta kama majalisar dokokin kafin ayi zaman yau.
Maganar Tolu Ogunlesi a Twitter
"Laifin mene ya aikata da ya cancanci a tsige shi tun da ya hau kan karagar mulki?
Me majalisar dokoki ta ke cewa ya aikata? Tsige (gwamna) ba abu ne da ake yi saboda ganin dama ba.
Sannan kuma ba a shekarar 2003 ko 2006 mu ke ba.
Ban san Gwamnan nan ba kuma ban tunani na damu da siyasar Ribas, amma ya kamata a fadi wannan: Idan majalisar Ribas ta cigaba da irin wannan hara-gido irin na zamanin Obasanjo, ba za ta yi nasara a kotu ba.
Fubara zai bi sahun Peter Obi "
- Tolu Ogunlesi
Fubara: Shawarar Tomide Akinribido
Tsohon ‘dan majalisar Ondo, Hon. Tomide Akinribido ya ba Fubara shawara a Twitter ya nemi mafita idan ‘yan majalisarsa ba su tare da shi.
Akinribido ya na ganin muddin aka samu mutum 24 da ke tare da Nyesom Wike, sun kai adadin da za su iya tunbuke gwamna a tsarin mulki.
Majalisar Ribas ta kori Edison Ehie
Alamu na nuna akwai sabani tsakanin Gwamnan Ribas da uban gidansa a siyasa, Nyesom Wike, ana da labari an sauke Edison Ehie.
Idan mutanen Wike a majalisar dokoki su ka samu yadda su ke so, za a kori Fubara daga kan mulki, bai kai wata shida da shiga ofis ba.
Asali: Legit.ng