An Fara Rabawa Kowane ‘Dan Majalisa 'Jeep' Mai Numfashin Fiye da Naira Miliyan 100
- A lokacin da ake yawan kukan yadda rayuwa ta yi tsada a yau, za a gwangwanje ‘yan majalisar tarayya ne da motoci
- Dirka-dirkan motocin da za a rabawa ‘yan majalisar wakilai da sanatoci zai ci makudan biliyoyi, hakan ya jawo suka
- Majalisa ta ce akwai bukatar a samu katuwar mota da ‘dan majalisa zai ji dadin aiki, an nuna aro za a ba ‘yan siyasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Motocin da aka sayowa ‘yan majalisar wakilan tarayya sun fara shigowa hannunsu duk da korafin facaka da ‘yan Najeriya su ke yi.
Rahoton da Punch ta fitar a yau ya tabbatar da cewa ‘yan majalisar wakilan su na karbar wadannan motoci na darurwan miliyoyi daga waje.
Sanatoci za su fara karbar na su motocin ne a makon da za a shiga, zuwa Disamba ana sa ran kowane ‘dan majalisa ya samu sabuwar mota.
'Yan majalisa za su samu motocin aiki
Kowane ‘dan majalisa zai samu mota kirar ‘Jeep’, sannan za a rabawa shugabannin da ke majalisar kasar motocin da harsahi ba su iya ratsa su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A matsayinsa na mai magana da yawun majalisar wakilai, Akin Rotimi ya sanar da jaridar cewa motocin sun soma shiga hannun abokan aikinsa.
Hon. Akin Rotimi ya ce an fi maida hankali ne ga matan da ke majalisa, masu nakasa da kuma ‘yan majalisan da ba a shari’a da su a kotun zabe.
Za a gujewa matsala a rabon motoci
Shugabannin majalisar sun yi hakan ne saboda gudun a samu matsala, a ba ‘dan majalisa motar miliyoyi sai daga baya kotu ta tsige shi daga ofis.
Sabon ‘dan majalisar da za a rantsar bayan watanni zai bukaci a ba shi motar aiki.
"Ba za a saida motocin ba" - Majalisa
A baya, ‘dan majalisa ya na iya karbar motarsa kuma ya saida, wannan karo an haramta yin hakan domin motocin mallakar majalisar tarayya ne.
Motocin za su iso ne sannu a hankali, za a fara da na shugabannin kwamitoci da ake da su.
'Yan majalisa su na shan sukar jama'a
Matakin nan da ‘yan majalisan tarayyar su ka dauka ya jawo suka da talakawan da su ke wakilta, mafi yawan mutane na kukan tsadar rayuwa.
Bayan janye tallafin man fetur da sakin farashin kudin kasashen waje a kasuwa, rayuwa ta kara yi wa jama’a tsada baya ga tashin farashi.
Asali: Legit.ng