Malamin Addini Ya Hango Gagarumin Matsala a Jihar Ondo, Ya Ce Gwamna Akerodlu Na Bukatar Addu'a

Malamin Addini Ya Hango Gagarumin Matsala a Jihar Ondo, Ya Ce Gwamna Akerodlu Na Bukatar Addu'a

  • Har yanzu tsugune bata kare ba tsakanin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa da yan majalisar dokokin jihar
  • Domin kwantar da hankalin gwamnan da ke fama da rashin lafiya, Aiyedatiwa ya nisanta kansa daga duk wata zanga-zanga game da zaman Gwamna Akeredolu a Ibadan, jihar Oyo
  • Wani malamin addini, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya saki wani bidiyo inda ya ce rikicin da ya dabaibaye jihar ta kudu maso yamma zai kara tsanani

Akure, jihar Ondo - Shahararren malamin addini Primate Elijah Ayodele, ya ce ya hango gagarumin rikici na siyasa a jihar Ondo.

Primate Ayodele ya nemi a taya gwamnan Ondo da addu'a
“Na Hango Rikicin Siyasa a Ondo”: Malamin Addini Ya Ce Gwamna Akeredolu Na Bukatar Addu’a Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Primate Ayodele ya hango matsaloli a siyasar Ondo

Shugaban cocin na INRI Evangelical ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a soshiyal midiya a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Za a Biya Nnamdi Kanu Naira Biliyan 8 Bayan Kotu Ta Soke Haramcin Kungiyar IPOB

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Allah ne kadai zai taimakeka kada a tsige ka daga mulki. Kuma Allah ne kadai zai dawo da Akeredolu. Lafiyar Akeredolu ba za ta daidaita ba a karshen mulkinsa. Sannan bayan wa'adin mulkinsa, zai kuma fuskanci abubuwa da dama."

Da yake ci gaba da bayani, Ayodele ya ce:

"Za a sha dirama iri-iri, a siyasance a jihar Ondo. Yunkurin kisan kai, kungiyoyin adawa za su yaki mataimakin gwamnan. Sannan kuma muna da kungiyoyin adawa na matar gwamna, za mu samu kungiyoyin adawa da aka nada, muna da kungiya daban-daban. Jihar Ondo ta dauki zafi a yanzu haka.
"Muna bukatar addu'a, idan ba haka ba za a samu matsaloli da dama."

Zan kammala mulkina a raye" - Akeredolu

A gefe guda, Legit Hausa ta kawo a baya cewa gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya koma bakin aiki bayan dogon hutun jinya da ya tafi a kasar Jamus.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

A ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba ne Akeredolu ya dawo gida Najeriya daga Jamus inda ya shafe watanni uku yana jinya. Gwamnan ya samu tarba daga makusantansa a gidansa da ke Ibasan, babban birnin jihar Oyo.

A ranar Juma'a, Akeredolu ya gana da masu ruwa da tsaki daga jihar ciki harda Olamide Oladiji, kakakin majalisar dokoki na jihar, Lucky Aiyedatiwa, mataimakin gwamna da mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a gidansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng