“Ka da Ka Mai da Mu Zamanin Jahiliyya”, Kotun Koli Ta Wancakalar da Atiku Kan Sabbin Korafe-Korafe

“Ka da Ka Mai da Mu Zamanin Jahiliyya”, Kotun Koli Ta Wancakalar da Atiku Kan Sabbin Korafe-Korafe

  • Kotun koli ta gargadi Atiku kan kokarin mayar ‘yan Najeriya baya a hukuncin da ake na zaben shugaban kasa a Abuja a yau Alhamis
  • Kotun ta ce wannan kokari na Atiku na sake shigar da wasu korafe-korafe zai kara yawaita tsawon lokaci na yanke hukuncin shari’ar da ake yi
  • Mai Shari’a, John Inyang Okoro wanda shi ne shugaban alkalan guda bakwai ya yi fatali da shirin na Atiku inda ya ce ba za su amince ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja – Kotun koli ta dakatar da kokarin shigar da wasu korafe-korafe na kalubalantar zaben Tinubu da Atiku ke shirin yi.

Mai Shari’a, John Inyang Okoro wanda shi ne shugaban alkalan guda bakwai ya ce kokarin kawo sabbin korafe-korafe kan Tinubu game da takardun Tinubu zai kara tsawaita shari’ar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

“Babu rana”: Gwamnatin Kano ta magantu kan lokacin da kotu zata yanke hukuncin zaben Abba Gida-Gida

Kotun koli ta caccaki Atiku kan kokarin mayar da su baya a shari'ar
Kotun koli ta yi fatali da shirin Atiku na karo sabbin korafe-korafe. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Meye kotun koli ta ce kan Atiku na sabbin korafe-korafe?

Ya ce hakan zai kara mayar da kasar baya na shekarun jahiliyya inda ya ce kotun ba ta da hurumin karbar sabbin korafe-korafen, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Abin takaici ne yadda mu koma baya har lokacin jahiliyya wanda za a saurari korafe-korafen zabe har zuwa lokacin da shugaban da ake kalubalanta zai gama mulkinsa.”

Ya kara da cewa kokarin Atiku na shigar da wasu shaidu zai kara yawaita lokacin yanke hukuncin kotun zaben shugaban kasar.

Legit Hausa ta ji martanin mutane wannan lamari na kotun koli

Adamu Umar ya ce ya kamata Atiku kawai ya koma ga Allah saboda lokaci ya na kure masa.

Aishatu Abubakar ta ce:

"Duk da ba son shi kansa Tinubun na ke yi ba, amma naji dadi da aka yi fatali da korafe-korafen Atiku."

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan APC a jihar Arewa

Idris Yahaya ya ce Allah wadaran wannan kasa ta mu ta Najeriya wacce babu adalci a cikinta.

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Tinubu

A wani labarin, Kotun koli ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar.

Kotun har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam'iyyar LP.

Atiku da Obi sun kalubalanci nasarar Tinubu a zaben da aka gudanar a watan Faburairu na farkon wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.