Kotun Koli Ya Ruguza Manyan Hujjojin Atiku da Obi Wajen Tabbatar da Nasarar Tinubu

Kotun Koli Ya Ruguza Manyan Hujjojin Atiku da Obi Wajen Tabbatar da Nasarar Tinubu

  • Kusan duk wasu hujjojin karar zaben 2023 da Atiku Abubakar da Peter Obi su ka gabatar ba su yi wani tasiri a gaban kotu koli ba
  • Alkalan babban kotun kasar sun yi watsa-watsa da abubuwan da lauyoyin ‘yan takaran jam’iyyun hamayya su ka gabatar masu
  • Ba a karbi bayanan da Atiku ya samo daga baya a jami’ar CSU ba, a karshe an tabbatar da hukuncin kotun sauraron karar zabe

Abuja - Kotun koli ta saurari karar da Atiku Abubakar da Peter Obi su ka daukaka a kan zaben shugaban kasa da aka yi a Fabrairu.

A karshe kotun ta yi kaca-kaca da hujjojin da ‘yan takaran na jam’iyyun adawa su ka fake da su wajen kalubalantar nasarar Bola Tinubu.

The Nation ta ce Alkalan sun hadu a kan cewa babu inda doka ta wajabta samun 25% na kuri’un Abuja kafin ‘dan takara ya samu mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Kotun koli
Bola Tinubu ya yi nasara a kotun koli Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Kotun koli a kan 25% na kuri'un Abuja

Peter Obi da ya tsaya a jam’iyyar adawar LP ya zo na farko a Abuja, ya ce Bola Tinubu da APC ba su samu 25% a birnin tarayyar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da sashe na 134 na doka ta ce shi ne mai neman takara ya tashi da akalla 25% a kaso biyu bisa uku na jihohin 36 da kuma Abuja.

Mai shari’a John Okoro ya rusa karar Chris Uche, SAN a madadin Atiku Abubakar na cewa ba a aika sakamakon zaben ta na’ura ba.

IREV ba na'urar tattara sakamako ba ce - Kotun koli

Jaridar ta ce Kotun koli ta ce gazawar na’urar IREV ba ta nufin daina tattara sakamako.

Alkalan da su ka yi hukuncin sun ce rashin aikin IREV ba zai yi sanadiyyar da masu kada kuri’a za su samu wani rashin gamsuwa ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam’iyyar LP Ta Sha Gagarumin Alwashi Gabannin Hukuncin Kotun Koli

Hujjojin Atiku a kan digirin Tinubu

Da aka zo batun hujjojin da Atiku Abubakar ya samo daga jami’ar jihar Chicago watau CSU da Tinubu ya halarta, a nan ma PDP ba ta dace ba.

Alkalan sun ce ba za su karbi danyen hujjoji ba domin lokacin gabatar da hujjoji da doka ta tanada ya wuce, ba za a bankara tsarin mulki ba.

Su wanene su ka yi hukunci a kotun koli?

Ana da labari an zabo kwararrun Lauyoyi har da wanda su ka yi aiki a kasar waje kan batun shari’ar Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi.

John Inyang Okoro wanda ya fara aikin shari’a shearu 37 ya jagoranci sauraron shari’ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel