Hanyoyin Sata Mu Ka Toshe, Mu Ka Samu Kudin Yin Ayyuka Inji Abba Gida Gida

Hanyoyin Sata Mu Ka Toshe, Mu Ka Samu Kudin Yin Ayyuka Inji Abba Gida Gida

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nanata cewa a lokacin da aka damka masa mulki, bai samu wasu kudi a cikin baitul-malin jihar Kano ba
  • Abba Gida-Gida ya ce amma a yanzu, gwamnatinsa ta na yi wa talakawanta ayyuka ba tare da kukan karanci ko rashin kudi ba
  • Malam Bashir Ibrahim Na'iya ya wallafa bidiyon wannan jawabi da Gwamnan ya gabatar a kan shafinsa na Facebook a ranar Asabar

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi bayanin halin da ya tsinci gwamnati da irin matakan da ya dauka a mulkinsa.

A wajen wani taro da aka shirya a karshen makon jiya, an ga Abba Kabir Yusuf a bidiyo ya na cewa ya samu baitul-mali babu kudi a ciki.

Mai girma Gwamnan jihar Kano yake cewa ya toshe kofofin sata, a haka ya samu kudin da ya ke yi wa al’ummar da su ka zabe shi aiki.

Kara karanta wannan

Hakikanin Abin da Ya Faru – Gwamna Ya Yi Bidiyon Karyata 'Harin' da Aka Kai Masa

Abba Gida Gida
Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnatin Abba ta ce aiki za ayi wa Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ja-kunnen wadanda ya ba mukami cewa ba handamar kudin talakawa ya kawo su ba, sun zo gyara jihar ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun kwanakin baya aka ji gwamnatin NNPP mai mulkin jihar Kano ta dakatar da shugaban hukumar KASCO, Dr. Tukur Dayyabu Minjibir.

A cewar Abba Gida Gida, ya gaji bashin kusan Naira biliyan 400 amma duk da haka ya ce gwamnati ta dauko aiki a bangarori dabam-dabam.

Jawabin Gwamnan jihar Kano

"Mun tarar da gwamnati babu ko kobo, mun tarar da gwamnati da bashi, amma cikin ikon Allah, yau ga shi duk abin da mu ke so mu yi, mu na yin sa a jihar Kano.
Wannan ya na da nasaba hanyoyin na sace-sace a cikin harkokin gwamnati na babu gaira-babu dalili. Al’umma su na cikin kangi, talakawa na wahala, wasu tsiraru su na sace kudin al’umma, su na fita kasashen waje.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Mun tabbatar da cewa kudinku ba na mu ba ne, dole mu alkinta maku kudinku, mu yi maku abin da ya kamata.
Ina sake fada, duk wani wakilin gwamnati, wanda yake zaton ya shigo wannan gwamnatin ne domin ya yi sata, ina kara fada, to don Allah, don Annabi ya fita ya ba mu wuri, domin mu ba 'barayi bane, kuma baza mu bari a yi sata ba....."

- Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Kano ta kai shugaban KASCO kotu

Ku na da labari gwamnatin Kano ta yi karar Bala Inuwa Muhammadu a kotu cewa ya taba asusun hukumar samar da kayayyakin gona.

Binciken da PCACC ta gabatar ya nuna mata wanda ake tuhuma ya wawuri N4bn daga KASCO, kuma ya ba wasu jami’ai cin hancin N15m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng