Kai Tsaye: Kotun Koli Ta Fara Sauraron Daukaka Karar Atiku, Obi Kan Nasarar Tinubu

Kai Tsaye: Kotun Koli Ta Fara Sauraron Daukaka Karar Atiku, Obi Kan Nasarar Tinubu

A yau Litinin 23 ga watan Oktoba ne kotun ƙoli za ta saurari ƙararraki uku da ke ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa, wacce ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Masu shigar da ƙara su uku, Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma Allied Peoples Movement (APM), suna son kotun koli ta soke hukuncin kotun zaben shugaban ƙasa da ta tabbatar da nasarar Tinubu a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Kotun koli na sauraron daukaka karar Atiku, Peter Obi
Kotun koli na sauraron daukaka karar Atiku, Peter Obi kan nasarar Tinubu Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP, Olukayode Jaiyeola/NurPhoto, Nigerian Presidency/Handout/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Kotun ƙoli ta ɗage ɗaukaka ƙarar PDP/LP

Kotun ƙoli mai alƙalai bakwai a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Okoro ta dage zaman bayan ƙarar bayan muhawarar lauyoyin PDP da LP.

"Wannan ɗaukaka ƙarar an tanada hukunci har zuwa ranar da za a sanar da bangarorin," A cewar Okoro.

Kotun koli ta tanadi hukunci a ƙarar Obi/LP

Kotun ƙoli ta tanadi hukunci a ƙarar da Peter Obi da jam'iyyar Labour (LP) suka shigar. Mai shari’a Okoro ya ce za a sanar da ɓangarorin biyu idan hukunci ya kammalu.

Lauyan wadanda suka shigar da ƙara, Livy Uzoukwu (SAN), yayin da yake gabatar da rubutaccen bayaninsa, ya roki kotun da ta amince da buƙatun da suka nema a ƙarar.

Lauyoyin masu kare waɗanda ke ƙara, Abubakar Mahmoud (SAN) na INEC, Wole Olanipekun (SAN) na Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettma da Akin Olujinmi (SAN) na jam'iyyar APC sun buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta.

Kotun koli ta yi watsi da ƙarar da APM ta ɗaukaka

Kotun ƙoli ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta shigar.

Ƙarar dai tana ƙalubalantar zaɓen Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Kotun da Okoro yake jagoranta ta yi watsi da ƙarar bayan lauyan wanda ya shigar da kara, Chukwuma Majukwu Umeh, ya nemi janye karar.

Kotun ta kuma yi nuni da cewa ƙarar ba ta da tushe balle makama domin a baya kotun ƙoli ta yi hukunci a shari'ar DP da INEC da sauransu, mai cewa an bi ƙa'ida wajen zaɓo Kashim Shettima.

Kotu ta fara sauraron ƙarar jam'iyyar APM

Kotun ƙoli ta sake dawowa domin saurarin ɗaukaka ƙarar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta yi.

Kotu ta tanadi hukunci kan karar Atiku/PDP

Kotun koli ta tanadi hukunci a kan ƙarar da Atiku da PDP suka shigar.

Kotun mai alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Okoro, ta sanar da matakin ne bayan lauyoyin da ke kare ɓangarorin gabatar da bayanansu na ƙarshe.

Legit.ng ta tattaro cewa kotun ƙolin ta kuma saurari mahawara daga lauyoyin ɓangarorin a kan buƙatar da masu ɗaukaka ƙara suka shigar na kawo sabbin shaidu.

Tawagar lauyoyin Atiku a ƙarƙashin jagorancin Chris Uche (SAN), ta bukaci kotun da ta amince da bukatar ta da kuma soke cancantar Shugaba Tinubu.

Lauyoyin da waɗanda ake ƙara, Abubakar Mahmoud, SAN (INEC), Cif Wole Olanipekun, SAN (Tinubu) da Cif Akin Olujinmi, SAN (APC) sun buƙaci kotun da ta yi watsi da buƙatar da ɗaukaka ƙarar saboda rashin cancanta.

Ganduje, Ribadu, Gbajabiamila sun hallara a kotun koli

Yayin da ake shirin fara sauraran kararrakin zaben shugaban kasa, shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya samu halartar kotun.

Sauran wadanda su ka hallara a kotun sun hada da mai ba da shawara a harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila da sauransu.

Sauran

Kotun koli ta fara sauraron ƙara

Kotun Koli a yanzu ta fara sauraron ƙararraki uku da ke ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.

Kotun ƙolin ta fara da sauraron ɗaukaka ƙarar Atiku Abubakar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Mai shari’a John Okoro ne ke jagorantar alƙalai bakwai na kotun ƙolin da ke sauraron ƙararrakin.

Manyan lauyoyi sun iso kotun koli a Abuja

Manyan lauyoyi sun samu isowa zuwa kotun koli don fara shirin sauraran kararrakin zaben shugaban kasa.

Manyan lauyoyin sun hada da ma su kare jam'iyyar PDP da APC da kuma APM.

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel