Yan Siyasa 3 Da Suka Shafe Sama Da Shekaru 8 a Kan Kujerar Gwamna a Najeriya
- Wasu gwamnoni sun yi fiye da shekaru takwas da dokar kasa ta kayyade a matsayin wa’adin zababbun masu mulki
- Daga cikin ‘yan siyasar da hakan ta faru da su akwai Ibrahim Gaidam wanda ya yi mulkinsa tun daga 2009 har zuwa 2019
- Jolly Nyame da Bukar Abba Ibrahim sun zama gwamnoni a lokacin mulkin soja, da aka dawo farar hula su ka sake mulki
Abuja - Daga lokacin da aka fara siyasar farar hula a tarihi zuwa yanzu, an yi wasu gwamnonin da su ka yi sa’a, aka rantsar da su har sau uku.
Bayan an dawo farar hula a mulkin sojan Janar Ibrahim Badamasi Babangida a 1991, ‘yan siyasa sun shiga takara a karkashin jam’iyyun SDP da NRC.
Wasu daga cikin wadanda su ka yi mulki a wancan lokaci kafin zuwan Janar Sani Abacha, sun sake yin takara a jihohinsu da sojoji su ka bar mulki.
Gwamna ya mutu, mataimaki ya hau
A dalilin rasuwar shugaba, wasu mataimakan su kan yi sa’a a rantsar da su a kan kujera, daga baya kuma sai su nemi takara da kan su, su ci zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta kawo jerin ‘yan siyasar da su ka yi sama da shekaru takwas a kujerar gwamna.
1. Gwamna Jolly Nyame
Rabaren Jolly Nyame ya yi takarar Gwamna a Taraba a 1992 kuma ya yi nasarar lashe zabe, sai dai ba a dade ba, sojoji su ka sake komawa mulki.
A 1999 har wa yau, Nyame ya tsaya neman Gwamna a inuwar PDP ya sake samun nasara kamar yadda aka yi a 2007 da ya zarce a karo na biyu a jere.
2. Gwamna Bukar Abba Ibrahim
Jim kadan da kirkirar Yobe a matsayin jiha daga tsohuwar Borno, Bukar Abba Ibrahim ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar SDP, ya yi mulki a 1992.
Bayan ya bar ofis a Nuwamban 1993, sai Bukar Abba ya sake shiga takara sau biyu a jere a APP da ANPP, ya bar karagar mulki ne a watan Mayun 2007.
3. Gwamna Ibrahim Gaidam
A jihar Yoben ne kuma aka rantsar da Ibrahim Gaidam a matsayin gwamna a Junairun 2009 a sakamakon rasuwar Mai girma Mamman B. Ali.
Da aka zo zaben 2011 sai ANPP ta sake tsaida Ibrahim Gaidam, haka aka yi a 2015 wanda hakan ya ba shi damar zama gwamna a karo na uku a jere.
Za a karbe kujerar Gwamnan Kano?
Kwanaki kun ji labari Abba Kabir Yusuf ya garzaya kotu domin ya cigaba zama a kan kujerar Gwamna a Jihar Kano bayan kotun zabe ta tunbuke shi.
Wannan karo, Wole Olanipekun SAN wanda ya kware a shari’ar zabe ne sai kare Abba Gida Gida a kan APC da Nasiru Gawuna da aka ba nasara.
Asali: Legit.ng