Kotu Ta Tsige Sylva, Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Bayelsa

Kotu Ta Tsige Sylva, Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Bayelsa

  • Kotun Abuja ta yanke hukunci a shari'ar takarar Timipre Sylva, a matsayin dan takarar gwamnan APC
  • Yan makonni kafin zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023, babbar kotun tarayya, ta tsige Sylva
  • Hakan na zuwa ne yan makonni bayan APC a jihar Bayelsa ta tarbi tarin mambobin jam'iyyar PDP da Labour Party a inuwarta

FCT, Abuja - Wani rahoto da ke zuwa ya bayyana cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Timipre Sylva, daga yin takara a zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban.

Babbar kotun tarayyar ta yanke hukuncin ne a daren ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Dino Melaye Ya Gamu Da Gagarumin Cikas Yayin da Jiga-Jigan PDP Suka Sauya Sheka Wata 1 Kafin Zabe

Kotu ta dakatar da dan takarar APC a zaben gwamnan jihar Bayelsa
Kotu Ta Tsige Sylva, Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Bayelsa Hoto: Timipre Marlin Sylva
Asali: Facebook

Dalilin da yasa kotu ta tsige dan takarar gwamnan APC

Jaridar ThisDay ta rahoto cewa da yake yanke hukunci, Mai shari'a Donatus Okorowo, ya riki cewa zai zama take kundin tsarin mulkin 1999 idan aka bar Sylva ya yi takara, tunda an taba rantsar da shi sau biyu kuma ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar na shekaru biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya kuma ayyana cewa Sylva, dan takarar na jam'iyyar APC, bai cancanci yin takara a zaben ba saboda idan ya ci zabe kuma aka rantsar da shi zai shafe fiye da shekaru takwas a karagar mulki a matsayin gwamnan jihar.

Da yake misali da lamarin Marwa da Nyako a kotun koli, Okorowo ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana cewa kada a zabi wani mutum a matsayin gwamna fiye da sau biyu kuma cewa jam'iyyun da ke shari'ar sun yarda cewa an zabi Sylva sau biyu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Babban Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa Tsagin Adawa

Ya ci gaba da bayyana cewa idan aka bar Sylva ya yi takara a zabe mai zuwa, hakan na nufin mutum na iya takara iya adadin da yake so.

Hakan na zuwa ne bayan APC ta yi ikirarin cewa babu baraka a cikin sansaninta gabannin zaben na jihar Bayelsa kuma cewa duk masu ruwa da tsaki a jihar suna kan tafarki daya na kawowa dan takarar jam'iyyar, Sylva nasara a zaben, rahoton Daily Trust.

Zaben Kogi: Manyan jiga-jigan PDP sun yi watsi da Dino Melaye, sun koma APC

A wani labarin kuma, mun ji cewa Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa a jihar Kogi, ya hadu da gagarumin cikas wata daya kafin zaben.

Hakan ya kasance ne bayan manyan jiga-jigan PDP a jihar Kogi sun fara barin jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC yan kwanaki kafin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng