Badakalar Chicago: Keyamo Ya Bayyana Abin Da Atiku Zai Yi Don Nuna Tinubu Ya Kirkiri Takardar Bogi

Badakalar Chicago: Keyamo Ya Bayyana Abin Da Atiku Zai Yi Don Nuna Tinubu Ya Kirkiri Takardar Bogi

  • Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo ya ce Atiku ba shi da hanyar da zai iya tabbatar da cewa shedar karatun Tinubu ta bogi ce har sai wanda ya chanja shedar ya fito ya bayyana cewa shedar karya ce
  • Keyamo ya jaddada cewa hanyar da kawai za a bi shine dole Atiku ya nemo wanda ya bada shedar karatun don tabbatar da zarginsa
  • Bugu da kari, Keyamo ya bayyana kalaman da Atiku yayi a taron manema labarai a matsayin abin kunya, ya na mai cewa hakan na nuna siyasarsa ta kare

FCT, Abuja - Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama da cigaban sararin samaniya, ya ce dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ba zai iya gamsar da cewa shedar karatun Tinubu ta bogi ba ce har sai ya nemo wanda ya chanja shedar ya kuma tabbatar ta bogi ce.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Sanata ya ce mulkin Tinubu ya dace da Najeriya, ya fadi dalilai

Shaidar kammala karatun shugaba Tinubu ya zama abin cece-kuce a kokarin abokan hamayyarsa a 2023 na ganin sun karbi kujerar a kotu.

Keyamo ya fadi abin da Atiku zai yi don nuna Tinubu ya kirkiri satifiket
Badakalar Chicago: Keyamo Ya Bayyana Abin Da Atiku Zai Yi Don Nuna Tinubu Ya Kirkiri Takardar Bogi. Hoto: @Atiku @OfficialABAT
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Najeriyar ya karbi shedar kammala jami'ar Chicago Jihar Chicago (CSU) bayan kammala makarantar.

Rajistaran makarantar CSU, Caleb Westberg, ya bayyana cewa ana iya bada sabon shedar kammala karatu, amma wanda aka bayar a 1997 jami'ar ce ta bada shi.

Atiku wanda shine dan takarar PDP zaben 2023 ya shigar da kara a gaban wata kotun Amurka kan yana bukatar tarihin karatun Tinubu, bisa zargin shaidar bogi ce da Tinubu.

Ya kuma daukaka kara yana kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe tare da bukatar gabatar da shedar karatun Tinubu a matsayin sabuwar shaida.

Duk wanda ya yi ikirari sai ya bada tabbaci, cewar Keyamo

Da yake sharhi a dandalin sadarwa ta X ranar Lahadi, 8 ga Oktoba, Keyamo ya ce dole Atiku ya nemo wanda ya sake bawa Tinubu sabuwar shaida don tabbatar da sahihanci ko akasin haka.

Kara karanta wannan

Takardun Tinubu: “Kai Ta Shafa, Babu Ruwan Kwankwaso Da Karar Da Ka Shigar”, NNPP Ga Atiku

Ya ce ikirarin Atiku "ba shi da amfani" har sai wanda ya bada sakamakon ya bayyana rashin ingancin.

"Kuma hakkin wanda ke da tuhuma ne ya nemo wanda ya bada sakamakon a matsayin shaida. Ba wai wanda ake tuhuma ba. Wanda ya yi ikirari dole ya bada hujja.
"Wannan wata hanya ce da nayi amfani da ita lokacin da muke kare nasarar Buhari a 2019 da suka dinga murna kamar sun yi nasara" a cewar babban lauyan.

Ta karewa Atiku a siyasa, cewar Keyamo

Ranar Alhamis, 5 ga Oktoba, Atiku ya yi taron manema labarai inda ya bayyana abin da lauyoyinsa suka gano a tarihin karatun Tinubu da aka ba su.

Sai dai, Keyamo ya bayyana kalaman Atiku a matsayin kame-kame, ya na mai cewa hakan na nuna ta kare masa a siyasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel