Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Uno Na Akwa Ibom

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Uno Na Akwa Ibom

  • An tabbatar da Fasto Umo Eno na jihar Akwa Ibom a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamna ranar 18 ga watan Maris, 2023
  • Kotun zaɓe mai zama a Uyo, babban birnin jihar ta kori kararrakin jam'iyyun ADC da NNPP da 'yan takararsu bisa hujjar rashin cancanta
  • Ɗan takarar ADC ya yi zargin cewa Kotun majistire ta kama Eno da laifi har ta hukunta shi amma Kotun zaɓe ta ce daga baya an soke hukuncin

Akwa Ibom - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna mai zama a Uyo ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Akwa Ibom.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, 2023, Kotun ta yi fatali da ƙarar jam'iyyar ADC da ɗan takararta, Ezekiel Nyaetok, waɗanda suka ƙalubalancin nasarar Gwamna Eno na PDP.

Kara karanta wannan

Kujerar Gwamnan PDP Ta Fara Tangal-Tangal, Kotun Zaɓe Zata Yanke Hukunci Kan Zaɓen Da Ya Lashe

Kotu ta yanke hukunci kan nasarar gwamnan Akwa Ibom.
Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Uno Na Akwa Ibom Hoto: Umo Eno
Asali: Twitter

Kotu ta kori karar ADC da NNPP

Tun da farko, Kotun ta kori ƙara mai lamba EPW/AKS/GOV/03/23, wacce jam'iyyar NNPP da nata ɗan takarar, Sanata John James Akpan Udoedehe, suka ƙalubalanci nasarar PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ƙorafin da ya gabatar, Nyaetok na jam’iyyar ADC ya roki kotun da ta kori Eno saboda wata kotun majistare da ke zama a Abuja ta kama shi da laifi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Nyaetok ya kuma kalubalanci sauran 'yan takarar da suka samu kuri'u fiye da shi a zaben da cewa suna fuskantar shari'a da dama, wanda hakan ya sa ba su cancanci tsayawa takara ba.

Meyasa Kotu ta tabbatar da nasarar Eno

Sai dai alkalin kotun mai shari’a Adekunle Adeleye, ya yanke cewa wannan kotun majistare da Emeka Iyama ya jagoranta ta soke hukuncin da aka yankewa Fasto Umo Eno tun da farko.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Kwace Ƙarin Kujerar Ɗan Majalisar PDP a Arewa, Ta Bai Wa APC Nasara

Daga nan Kotun ta yi watsi da karar Nyaetok bisa rashin cancanta, inda ta kara da cewa ya gaza tabbatar da cewa an saɓa wa dokokin zaɓe.

1 Ga Oktoba: Gwamnatin Kwara Ta Ce Ba Zata Yi Bikin Ranar Yancin Kai Ba

A.wani labarin na daban Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya ce gwamnatinsa ba zata gudanar da shagalin ranar 'yancin kai ba.

Kwamishinar yaɗa labarai, MisisBola Olukoju, ce ta tabbatar da haka ranar Alhamis, ta ce an yi haka ne saboda yanayin da mutane ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel