Kwankwaso Ba Zai Taba Zama Shugaban Kasa Ba, Inji Ganduje Yayin da Ya Tarbi Dan Takarar Gwamnan NNPP

Kwankwaso Ba Zai Taba Zama Shugaban Kasa Ba, Inji Ganduje Yayin da Ya Tarbi Dan Takarar Gwamnan NNPP

  • Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ba zai iya zama shugaban kasa ba
  • A cewar Ganduje, son zuciyar Kwankwaso ba zai bari ya cimma kudirinsa na son zama shugaban kasa ba
  • Ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi dan takarar gwamna na NNPP a jihar Bauchi wanda ya koma APC

FCT, Abuja - Abdullahi Ganduje, Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaben 2023 ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da dan takarar gwamna na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Bauchi, Haliru Dauda Jika, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

Jika ya samu tarba daga wajen Abdullahi Ganduje, a sakatariyar jam'iyyar na kasa da ke Abuja a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, rahoton Vanguard.

Dan takarar gwamnan NNPP a jihar Bauchi ya koma APC
Kwankwaso Ba Zai Taba Zama Shugaban Kasa Ba, Ganduje Yayin da Dan Takarar Gwamnan NNPP Ya Koma APC Hoto: Adam Haruna Bala
Asali: Facebook

Ganduje ya ce Jika ya gane cewa jam'iyyar yan Kwankwasiyya ta NNPP mayaudariya kuma maciya amana ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Guardian ta rahoto, yayin da yake tarbar Jika da kungiyarsa a APC, Ganduje ya cire masa jar hula ta Kwankwasiyya sannan ya maye gurbinsa da hula mai dauke da tambarin Tinubu.

Ya ce:

"Ya dawo jam’iyyar da ke da ci gaba da kuma mai da hankali idan muka kalli daga inda ya fito. Ya fito ne daga jam’iyyar da a baya ta kasance mai mutunci da ake ganin girmanta amma daga baya kungiyar Kwankwasiyya ta yi awon gaba da ita tare da gurbata ta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tsohon Minista a Najeriya Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

"Mun yi farin ciki da garin cewa ainahin jam'iyyar NNPP na gaskiya ta fara kwace matsayinta tare da tarwatsa kungiyar Kwankwasiyya da yin watsi da ita gaba daya."

Kwankwaso ya gwammaci zama "Sarki a wuta da ya zama bawa a Aljanna"

Ya bayyana cewa son zuciyar dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso zai ci gaba da kawo masa cikas a kudirinsa na son zama shugaban kasar Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce Kwankwaso ya gwammaci zama "Sarki a wuta da ya zama bawa a Aljanna."

Jogin jam’iyyar NNPP, Abbas ya zargi Kwankwaso kan rasa kujerar gwamna a jihar Kano

A wani labarin, mun ji cewa jwani jigon jam’iyyar NNPP, Alhaji Abbas Onilewura ya zargi Kwankwaso da bayar da gudunmawa wajen rasa nasarar jam’iyyar a jihar Kano.

A ranar Laraba 20 ga watan Satumba ne kotun zabe ta tsige Gwamna Abba Kabir na jam’iyyar a matsayin gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng