Ogun: Kotu Ta Daure Tsohon Ciyaman Din Da Ya Zargin Gwamna Da Kwashe Kudi

Ogun: Kotu Ta Daure Tsohon Ciyaman Din Da Ya Zargin Gwamna Da Kwashe Kudi

  • Kotu ta umarci a garƙame tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun a gidan gyaran hali
  • Hakan ya biyo bayan gurfanar da shi da hukumar 'yan sanda ta yi a gaban Kotun majistire mai zama a Abeokuta ranar Talata
  • Wale Adedayo, ya shiga tsaka mai wuya ne tun bayan lokacin da ya zargi gwamna Dapo Abiodun da karkartar da kuɗaɗe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Ogun ta gurfanar da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas, Wale Adedayo, a Kotun Majistire mai zama a Abeokuta.

Adedayo ya jawo ruwan dafa kansa ne yayin da ya zargi gwamna Dapo Abiodin na jihar Ogun da karkatar kasafin kananan hukumomi 20 da ke jihar na tsawon shekaru.

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas, Wale Adedayo.
Ogun: Kotu Ta Daure Tsohon Ciyaman Din Da Ya Zargin Gwamna Da Kwashe Kudi Hoto: Wale Adedayo
Asali: Twitter

Ya kuma miƙa ƙorafi ga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa (EFCC), inda ya roƙi hukumar ta binciki gwamna Abiodun na APC, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Matsalar da Adedayo ya shiga bayan ya zargi Abiodun

Jim kaɗan bayan haka, Kansilolin ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas suka dakatar da Ciyaman ɗin biyo bayan taƙalar ya yi wa mai girma gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka kuma hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta titsiye shi na tsawon kwanaki uku a ofishinta reshen jihar da ke Abeokuta, babban birnin Ogun.

A ranar 14 ga watan Satumba, 2023, kansiloli suka tsige Mista Adedayo daga matsayin shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas.

Jami’an ‘yan sanda sun kama shi a ranar Litinin a Ijebu-Ife inda suka kai shi hedikwatar ‘yan sanda da ke Eleweran, Abeokuta.

Hukumar 'yan sanda ta gurfanar da shi a Kotu

A ranar Talata, aka gurfanar da shi kan tuhuma biyu a gaban kotun majistare mai zama a Isabo, Abeokuta, biyo bayan ƙorafin da gwamnatin jihar ta rubuta.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Kyau Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a Zaɓen 2023

Sakataren gwamnatin Ogun, Tokunbo Talabi, ya rattaɓa hannu kan takardar korafin mai taken:

"Korafi kan Wale Adedayo bisa yaɗa karya da gangan, rahoton gwamnati na ƙarya, barazana ga rayuwa da tsoma baki wajen gudanar da ayyukan gwamnati."

Kotu ta tura tsohon Ciyaman ɗin gidan yari

A hukuncin da ya yanke bayan lauya ya nemi beli, mai shari’a A.K Araba, ya amince a bada belinsa kan kudi Naira miliyan 2 da kuma mutum biyu da zasu tsaya masa masu gaskiya da rikon amana.

Alkalin Kotun ya kuma gindaya cewa dole waɗanda zasu tsaya masa su kasance mazauna yankin da Kotun ke zama kuma sun mallaki kadara da shaidar biyan haraji.

Daga nan kuma ya umarci a tasa ƙeyar Mista Adedayo zuwa Kurkukun Ibara da ke Abeokuta har zuwa lokacin da za a cika sharuɗɗan beli, Vanguard ta rahoto.

Bayan haka Alkalin ya ɗage zaman zuwa ranar 20 ga watan Oktoba, 2023 domim fara sauraron shari'ar.

Kara karanta wannan

Shugabanni da Kusoshin Jam'iyya Sun Jingine Tsohon Gwamna, Sun Koma Inuwar APC

Tsohon Ministan Ayyuka, Onolememen, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

A wani rahoton kuma Babbar jam'iyyar adawa PDP ta ƙara shiga tasku yayin da tsohon Ministan ayyuka ya sanar da ficewa daga jam'iyyar a hukumance.

Chief Mike Oziegbe Onolememen ya tura wasiƙar fita daga PDP ga.shugaban jam'iyya na ƙasa da na jiharsa ranar 25 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel