Jigon NNPP Ya Yi Magana Kan Dakatar Da Kwankwaso Daga Jam'iyyar
- An yi Allah wadai da dakatarwar da aka yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Kwankwaso a zaben 2023 daga jam'iyyar
- Damilare Abioro, jigo a jam’iyyar NNPP, a wata hira da Legit.ng, ya tabbatar da cewa dakatarwar ba za ta tabbata ba, kuma Kwankwaso shi ne jagoran jam'iyyar na ƙasa
- Abioro ya cigaba da cewa ba zai yiwu a kauda kai kan tasirin gudunmawar Kwankwaso ga jam’iyyar NNPP ba, inda ya buƙaci jam'iyyar ta mayar da hankali wajen haɗin kai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abeokuta, Ogun – Damilare Abioro, jigo a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) daga jihar Ogun, ya yi Allah-wadai da dakatar da Rabiu Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Boniface Aniebonan, tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP, a ƙarshen watan Agusta, ya jagoranci wani bangare na jam’iyyar da suka dakatar da tsohon gwamnan Kano na tsawon watanni shida, bisa zargin cin dunduniyar jam'iyyar.
Me yasa NNPP ta dakatar da Kwankwaso
Aniebonan ya ƙara naɗa Manjo Agbo, tsohon sakataren watsa labaran NNPP na ƙasa a matsayin shugaban riƙo na jam'iyyar na kasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai Abioro, matashin ɗan takarar kujerar Sanata a jam’iyyar gabanin zaɓen 2023, yayin da yake tattaunawa da Legit.ng, ya ce abin da jam’iyyar ke bukata a yanzu shi ne hadin kai da kawo sabbin mambobi zuwa jam'iyyar maimakon dakatar da ƴaƴanta.
A cewar ɗan siyasar wanda haifaffen Idi-Iroko ne, ba za a iya ruguza tasirin da Kwankwaso ke da shi kan farin jinin da jam'iyyar ta samu gabanin zaɓen shugaban ƙasa a 2023 ba.
Rikicin NNPP: Abin da Abioro ya ce game da dakatar da Kwankwaso
A kalamansa:
"A matsayinsa (Kwankwaso) na jagoran jam'iyyar na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben da ya gabata, ya taimaka matuka wajen ci gaban jam’iyyar."
"Abin da jam’iyyar ke bukata a yanzu shi ne mutane su shigo cikinta, ko da muna sa ran mutane daga wasu jam'iyyun siyasa ne, dakatar da Dr Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam'iyyar ko korar ƴaƴan jam'iyya ba shi ne abin da ya dace ba."
Jigon NNPP Ya Zargi Kwankwaso
A wani labarin kuma, wani jigo a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya ɗora laifin rasa kujerar gwamnan Kano a kotu a kan Rabiu Musa Kwankwaso.
Jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Abbas Onilewura ya zargi dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso kan rasa nasarar jam’iyyar a jihar Kano.
Asali: Legit.ng