Rigima ba ta Kare ba, NNPP da Kwankwaso Za Su Gwabza a Kan Tambarin Jam’iyya

Rigima ba ta Kare ba, NNPP da Kwankwaso Za Su Gwabza a Kan Tambarin Jam’iyya

  • Wasu jagororin NNPP sun nuna babu ruwansu da kokarin da ake yi a canza tambarin jam’iyya
  • Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa su na shirin kawo canza a kundin tsarin mulkin NNPP
  • Peter Ogah ya sanar da hukumar INEC cewa wadanda su ka kafa jam’iyya ba su san da batun ba

Abuja - Jam’iyyar NNPP ta rubutawa hukumar INEC takarda a game da shirin da wasu su ke yi na canza tambarin da aka san ta da shi.

Vanguard ta kawo rahoto dazu cewa Peter Ogah ya rubuta wasika a madadin jam’iyyar wanda ta shiga hannun manema labarai a Legas.

Haka kuma jam’iyyar adawar ta kuma aika takarda zuwa ga Rabiu Musa Kwankwaso domin a janye yarjejeniyar da aka yi da Kwankwasiyya.

Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da shugabannin NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce Mista Peter Ogah ya zargi wasu marasa hurumi da neman canza masu tambari da tsarin mulki.

Kwankwaso ba su da hurumi a NNPP?

"Mu ne lauyoyin jam’iyyar NNPP, ta karkashin Dr Boniface Okechukwu Aniebonam wanda ya kafa ta da shugaban BOT, Dr Temitope Aluko, mu na rubuto wannan bisa umarninsu
Wadanda mu ke karewa a gaban shari’a sun ce wasu daidaikun mutane su na yunkurin canza tambarin jam’iyya kuma su canza doka, saboda haka dole mu fito da wannan sanarwa.
Ana sanar da hukumar a doka cewa wasu da ba su da iko su na wannan mugun tsari, saboda haka dole ayi watsi da wannan ko kuma ka da a saurari wanin canji da bai fito daga jam’iyya ba."

- Peter Ogah

The Nation ta ce Ogah a wasikarsa ya yi godiya ga hukumar INEC bisa bin dokar kasa da ta ke yi.

Yarjejeniyar Kwankwasiyya da NNPP

A game da ‘dan takaran shugaban kasa na 2023, takardar ta tuna masa yarjejeniyar da aka yi a Fabrairun 2022 tsakanin Kwankwasiyya da NNPP.

A cewar Ogah, jagororin NNPP sun godewa mabiya Kwankwasiyya da su ka hada-kai da su a zaben 2023, su ka ce yanzu Allah ya raka taki gona.

Yadda za a gyara zaben Najeriya

A ra’ayin Osita Chidoka, an ji ya na cewa bai dace a rika shari’ar sauraron karar zabe bayan an yi rantsuwa ba saboda ba za ayi adalci a kotu ba.

‘Dan siyasar ya na so a wajabta samun goyon bayan 50% a zabe kafin ‘dan takara ya karbi mulki, hakan zai kara farin jini da karbuwar shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng