'Yan Kasuwa Sun Rufe Shagunansu A Jihar Kano Bayan Yanke Hukuncin Kotu
- Hankula sun fara tashi yayin da kotu ta yanke hukuncin zaben gwamna a jihar Kano
- Mutane da dama sun rufe shagunansu a Kantin Kwari da Kasuwar Singa da sauran wurare
- Wannan na zuwa ne bayan kwace kujerar Gwamna Abba Kabir a yau Laraba 20 ga watan Satumba
Jihar Kano - Sa'o'i kadan bayan sanar da hukuncin kotu, 'yan kasuwa a jihar Kano sun rufe shagunansu zuwa gida.
Kotun ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir tare da tabbatar da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe a jihar, Legit ta tattaro.
Wasu wurare ne aka rufe shaguna da dama a Kano?
Daga cikin wuraren da aka rufe shagunan akwai Sabon Gari da Kantin Kwari da kuma Kasuwar Singa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust ta tattaro cewa hatta babban kanti na Ado Bayero a kulle ya ke kamar sauran wurare.
A yayin yanke hukuncin a Kano, kotun ta tabbatar cewa akwai kuri'u sama da dubu 165 wadanda ba a saka hannu ba wanda hakan ya saba doka da kuma nuna haramcinsu.
Me ake ciki yanzu haka a Kano?
A yanzu haka Kano ana cikin wani irin yanayi wanda ba a san me zai je ya dawo ba zuwa wayewar garin Alhamis 21 ga watan Satumba tun bayan yanke hukuncin kotu a jihar a yau dinnan.
Ana zaman dar-dar tsakanin magoya bayan jam'iyyar NNPP ta Abba Kabir Yusuf da kuma na bangaren jam'iyyar APC na Nasiru Gawuna wanda tsohon mataimakin gwamna ne.
Kafin yau Laraba, an sha samun hatsaniya tsakanin jam'iyyun biyu inda ko wane bangare ke zargin daya kan shari'ar da ke kotun.
Kotu ta kwace kujerar Abba Kabir, ta bai wa Gawuna
A wani labarin, Kotun sauraran kararrakin zabe ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP a yau Laraba yayin yanke hukuncin kotu.
Har ila yau, kotun ta kuma tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin zababben gwamnan jihar wanda ya kasance dan jam'iyyar APC mai mulki a kasar.
Bayan sanar da hukuncin kotun, mutane a birini Kano na zaman dar-dar musamman tsakanin magoya bayan jam'iyyar NNPP da kuma na APC.
Asali: Legit.ng