Tikitin Musulmi Da Musulmi: “Kana Fifita Yarbawa Da Kiristoci”, MURIC Ta Caccaki Tinubu Kan Mukamai

Tikitin Musulmi Da Musulmi: “Kana Fifita Yarbawa Da Kiristoci”, MURIC Ta Caccaki Tinubu Kan Mukamai

  • Shahararriyar kungiyar Musulunci ta caccaki gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagoranacin Bola Tinubu kan zabinta wajen nadin mukaman siyasa
  • Shugaban kungiyar kare hakkin Musulmai ya zargi Shugaba Tinubu da fifita Yarabwa da Kiristoci a nadin mukaman da ya yi zuwa yanzu
  • Babban daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bukaci Tinubu da ya yi daidaito wajen nade-nade masu zuwa,a gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha caccaka kan nade-naden mukaman siyasa da gwamnatinsa ta yi, yayin da aka yi masa tuni kan tikitin Musulmi-Musulmi wanda shi da mataimakinsa Kashim Shettima suke shugabanci a kai.

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da ganin cewa dukkan yankuna, addinai da sassa sun amfana daga nadin mukaman da gwamnatinsa sannan kada a fifita wata kabila ko addini sama da saura.

Kara karanta wannan

Kiristoci Sun Yi Amai Sun Lashe Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Sun Yabi Tinubu Kan Mukamai

MURIC ta yi wa Tinubu wankin babban bargo kan nade-nadensa
Tikitin Musulmi Da Musulmi: “Kana Fifita Yarbawa Da Kiristoci”, MURIC Ta Caccaki Tinubu Kan Mukamai Hoto: Ishaq Akintola, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Babban daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya yi wannan rokon ga Tinubu a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya zargi Tinubu da son kai wajen nade-nadensa inda ya nada Yarbawa da Kiristoci a manyan mukamai a gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Akintola ya ce:

“Mun yi matukar mamaki kan yadda Tinubu yake nada Kiristoci da Yarbawa a kan manyan mukamai tun farkon wannan gwamnati sama da Musulmai.
"An yi watsi da Musulmai da dama masu kwazo da suka yi yakin neman zabe kuma suka zabi tikitin musulmi da musulmi a lokacin zaben shugaban kasa."

Farfesa Akintola ya shawarci shugaban kasar da ya tabbatar da daidaito a nade-nadensa masu zuwa, SaharaReporters ta rahoto.

Kashim ya nada dan uwan Datti Baba-Ahmed a matsayin hadiminsa a harkokin siyasa

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Nada Muri-Okunola, Yakasai, Da Wasu 14 a Matsayin Hadimansa

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya na Hakeem Baba-Ahmed a matsayin hadimi bangaren siyasa ga mataimakinsa, Kashim Shettima.

Dakta Hakeem shi ne kakakin Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) kuma mai yawan sukar tsare-tsaren jam'iyyar APC mai mulki, Legit ta tattaro.

Hakeem ya kasance dan uwan Dakta Datti Baba-Ahmed, mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour. Wannan mukamin ya bai jama'a mamaki ganin yadda Hakeem ya ke zazzagar jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng