Gwamnatin Tinubu Na Kulla Yadda Za a Kama Ni a Tsare, Hadimin Atiku

Gwamnatin Tinubu Na Kulla Yadda Za a Kama Ni a Tsare, Hadimin Atiku

  • Makusancin Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ƙulla yadda za a damƙe shi a garkame
  • Daniel Bawal ya ce wasu sahihan bayanan sirri da ya samu daga Aso Villa, sun nuna ana shirin sa jami'an tsaro su yi ram da shi
  • Ya bayyana cewa yana nan kan bakarsa ta adawa da tikitin mabiya addini ɗaya wanda shi ne dalilin barinsa APC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Hadimin ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023, Daniel Bwala, ya tona shirin gwamnatin tarayya na kama shi da tsare shi.

Mista Bawala ya yi zargin cewa gwamnatin APC karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na ƙulle-kulle ta karkashin ƙasa kan yadda za ta sa a cafke shi a kulle.

Daniel Bawala da shugaba Tinubu.
Gwamnatin Tinubu Na Kulla Yadda Za a Kama Ni a Tsare, Hadimin Atiku Hoto: @BwalaDaniel, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Makusancin Atikun kuma Lauya masanin doka ya yi wannan zargi ne a shafinsa na manhajar X wacce aka fi sani da Tuwita ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

Yan Soshiyal Midiya Sun Taso Obasanjo a Gaba Bayan Ya Yi Wa Sarakuna Wani Abu 1 a Bainar Jama'a

Ya yi ikirarin cewa yana da sahihan bayanai daga wasu mutane a fadar shugaban kasa kan yadda ake shirin yin amfani da jami’an tsaro wajen kama shi tare da tsare shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bwala ya rubuta a shafinsa na X cewa:

"Jiya da daddare na samu bayanan sirri daga wasu ƙusoshin fadar shugaban ƙasa cewa gwamnati ta fara shirin amfani da jami'an tsaro su kama ni kuma su tsare ni a hannunsu."
"Ana kulla wannan makircin ne domin a ci mun mutunci kuma a rufe mun baki saboda na zame wa gwamnati mai ci ƙarfen ƙafa."
"Ya kamata yau duniya ta sani cewa ina nan kan baka ta na yaƙi da tikicin mabiya addini ɗaya wanda ta dalilin haka ne na fice daga jam'iyyar APC na koma tsagin Adawa. Idan wani abu ya faru ɗani duniya ta san shaiɗanun."

Kara karanta wannan

Shari’ar zabe, 50% da Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Zabe – Ministan Jonathan

Bwala na ɗaya daga cikin wadanda suka fice daga jam’iyyar APC bayan ta ayyana tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban ƙasa na 2023 da ya shuɗe.

Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Zabe

A wani labarin na daban Gwamna Dauda Lawal ya nuna jin daɗinsa dangane da hukuncin da Kotu ta yanke kan zaben gwamnan jihar Zamfara.

Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta tabbatar da nasarar Lawal na jam'iyyar PDP bayan ta ƙori karar Bello Matawalle na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262