Tsohon Gwamnan Jihar Neja Ya Nemi a Dakatar Da Fansho Da Alawus Dinsa
- Tsohon gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya bukaci gwamnatin jihar Neja da ta dakatar da fansho da alawus dinsa
- Sanata Sani Bello ya ce ya dauki matakin ne don yana ganin bai dace ya dunga cin moriyar fansho ba alhalin yana karbar albashi a majalisar dattawa
- Ya bukaci a ci gaba da dakatar da fansho din har zuwa lokacin da zai kammala wa'adinsa a matsayin sanata mai wakiltar Neja ta arewa
Jihar Niger - Tsohon gwamnan jihar Neja kuma sanata mai wakiltan Neja ta arewa a yanzu, Abubakar Sani Bello, ya bukaci a dakatar da fansho da sauran alawun da tsoffin gwamnonin jihar ke cin moriya.
Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, Sanata Bello ya bukaci hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa gwamnatin jihar.
Dalilin da yasa na nemi a dakatar da fansho da alawus dina, Sanata Sani Bello
Ya bayyana a cikin wasikar da ya aikewa Gwamna Mohammed Umar Bago, mai kwanan wata 6 ga watan Satumba, 2023, cewa ya dauki matakin ne bisa dalilai na da’a da kuma kyawawan dabi’u.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanata Sani Bello ya nemi a dakatar da fansho da alawus dinsa ne kasancewarsa sanata mai ci kuma ba zai yiwu ya dunga karbar fansho yayin da yake karbar albashi a majalisar dattawa ba.
Tsohon gwamnan ya ce a ci gaba da dakatar da fansho din nasa har zuwa lokacin da zai bayar da sanarwa sabanin haka bayan kammala wa'adinsa a matsayin sanata, rahoton Punch
Ya rubuta a wasikar:
"Ina mai rubuta wasikar nan don neman a dakatar da fasnho da alawus dina daga gwamnatin jihar Neja na iya lokacin da zan yi a matsayin sanara....
"Mai girma gwamna na iya tuna cewa an rantsar da ni a matsayin sanata mai wakiltar Neja ta arewa a majalisar dattawa ta 10 a ranar 13 ga watan Yunin 2023.
"Ina ganin bai dace ba a dabi'ance da da'ance na mori fansho da alawus dina a matsayina na tsohon gwamnan jihar Neja yayin da nake daukar albashi a matsayin sanata.
"Wannan dakatarwar ya ci gaba har sai na ba da sanarwar akasin haka bayan kammala wa’adina na Sanata."
An nemi Tinubu ya dakatar da Wike, Umahi da sauran tsoffin gwamnoni daga karbar fansho
A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar SERAP ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da ministocinsa, wadanda suka kasance tsoffin gwamnoni daga karbar kudin fansho daga jihohinsu.
Kungiyar mai zaman kanta ta yi kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng