Onyejeocha: An Zargi Ministar Tinubu da Kitsa Yadda Za a Tsige Shugaban Majalisa

Onyejeocha: An Zargi Ministar Tinubu da Kitsa Yadda Za a Tsige Shugaban Majalisa

  • A wani jawabi da aka alakanta da CAPW, an zargi Nkeiruka Onyejeocha da shiga siyasar ‘yan majalisa
  • Abidemi Johnson ta fito ta na cewa ministar ta bada kudi da nufin a tsige Tajudeen Abbas daga kujerarsa
  • Onyejeocha wanda yanzu ta bar majalisar wakilai, ta ce ‘yan adawa ne su ke yi mata sharri ba kowa ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wasu sun fito su na zargin Nkeiruka Onyejeocha da yunkurin tunbuke Rt. Hon Tajudeen Abbas daga shugabancin majalisar tarayya.

Leadership ta rahoto Hon. Nkeiruka Onyejeocha ta na cewa babu abin da ya hada ta da zargin da wasu su ke yi mata na shiga siyasar majalisa.

A wani jawabi da ta fitar ta ofishin babban sakataren yada labaranta, Gabriel Emameh, ministar kasar ta ce aikin da ke gabanta ya ishe ta.

Kara karanta wannan

"Mahaifina Ne Ya Jawo Min", Tsohuwa 'Yar Shekara 95 Da Ba Ta Taba Yin Aure Ba Ta Magantu, Bidiyon Ya Yadu

Shugaban majalisa
Nkeiruka Onyejeocha ta karyata shirin tsige shugaban majalisa Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Hon. Onyejeocha ta jefa kalubale

Onyejeocha ta kalubalanci masu zarginta da bada dalolin kudi domin a tsige Tajudeen Abbas su fito da hujjojin da za su tabbatar da gaskiyarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitacciyar ‘yar siyasar wanda ta yi shekaru 16 a majalisar tarayya ta yi raddi ga Abidemi Johnson, wanda ta fitar da jawabi da sunan wata CAPW.

Kungiyar CAPW ta matan da ke goyon bayan Tinubu ta ce karamar ministar ta raba kudi saboda ‘yan jarida su tasa shugaban majalisar kasar a gaba.

Jawabin Hadimin Ministan tarayya

"Wadannan karyayyaki ne daga abokan adawa da ba su san bambancin haske da duhu ba; abin da ya kamata da wanda bai dace ba.
Abin ban dariya ne sannan ya bukaci a gudanar da bincike na musmaman, Zargi ne marasa tushe wadanda ba su ba mu mamaki ba.

Kara karanta wannan

An Cire Takunkumi: Tinubu Ya Cin Ma Nasarori 3 Daga Zama Da Shugaban UAE

Mun samu labari kafin yanzu cewa ‘yan jarida za su huro mata wuta idan har ta samu nasara a kotun sauraron korafin zaben 2023."

- Gabriel Emameh

Emameh ya ce za a rika yin haka ne saboda idon ‘yan adawa ya rufe wajen ganin sun kai ta kasa, ta na cikin wadanda su ka yi nasara a kotun zabe.

Onyejeocha za ta koma Majalisa?

A makon jiya kotun sauraron karar zabe ta soke nasarar Amobi Oga a mazabar Isuikwuato/ Umunneochi, ta ba APC nasara a zaben majalisar.

A watan Agusta Bola Tinubu ya rantsar da tsohuwar ‘yar majalisar wakilan a matsayin karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng