Yadda jami’an ‘yan Sanda suka kashe wani dalibi lokacin da yake aikin neman kudi don ya biyawa kansa kudin makaranta – Majalisa

Yadda jami’an ‘yan Sanda suka kashe wani dalibi lokacin da yake aikin neman kudi don ya biyawa kansa kudin makaranta – Majalisa

- Majalisar Wakilai ta bayar da umurnin bincike game da kisan wani dalibi Ifeanyi Okafor, ya bisa ka’ida ba wanda jami’an ‘Yan Sanda sukayi sakamakon yaki bayar da cin hanci na N500

- Majalisar tace ‘Yan Sanda sun harbe Okafor a ranar 9 ga watan Fabrairu na shekarar 2018, a karamar hukumar Onuimo, dake jihar Imo

- Ciyaman na kwamitin kula da harkokin jiragen sama na majalisar, Mrs. Nkeiruka Onyejeocha, itace ta kawo shawarar a bincika lamarin don a hukunta masu laifin

Majalisar Wakilai ta bayar da umurnin bincike game da kisan wani dalibi Ifeanyi Okafor, ya bisa ka’ida ba wanda jami’an ‘Yan Sanda sukayi sakamakon yaki bayar da cin hanci na N500 wanda suka nema daga hannunsa.

Majalisar tace ‘Yan Sanda sun harbe Okafor a ranar 9 ga watan Fabrairu na shekarar 2018, a karamar hukumar Onuimo, dake jihar Imo.

Ciyaman na kwamitin kula da harkokin jiragen sama na majalisar, Mrs. Nkeiruka Onyejeocha, itace ta kawo shawarar a bincika lamarin don a hukunta masu laifin, inda tace ‘Yan Sandan sun tsayar da Okafor akan babbar hanya sun nemi cin hanci daga wajensa.

Punch Metro ta ruwaito daga majalisar a ranar Litinin cewa Onyejeocha ta bayyana zancan ne a gaban majalisar.

Yadda jami’an ‘yan Sanda suka kashe wani dalibi lokacin da yake aikin neman kudi don ya biyawa kansa kudin makaranta – Majalisa
Yadda jami’an ‘yan Sanda suka kashe wani dalibi lokacin da yake aikin neman kudi don ya biyawa kansa kudin makaranta – Majalisa

Inda tace “Abun haushi shine mahaifin yaron sakamakon bashi da hali ya shawarci yaronsa da yabi direban tifa don ya samu hada kudin makaranta, amma a kan hanyarsu ta Okigwe zasu kai kasa ‘Yan Sandan suka bukaci cin hancin N500, kawai don yaron yace basu da kudi kawai suka harbeshi.”

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC da dama sun sauya sheka zuwa PDP a Kaduna

Majalisar tace wannan lamarin ya sabawa sashe na 33 na dokar kasa ta shekarar 1999, wadda ta bawa ko wane dan Najeriya damar rayuwa.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa wata Lauya mazauniyar jihar Legas, Udeme Odibi, wadda aka ruwaito cewa ta dabawa mijinta wuka, Otike Odibi, har lahira, ta amsa laifinta na kisan kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel