Malamar Da'awa Naomi George Ta Ce An Yi Ma Ta Wahayi Peter Obi Ya Zama Shugaban Najeriya

Malamar Da'awa Naomi George Ta Ce An Yi Ma Ta Wahayi Peter Obi Ya Zama Shugaban Najeriya

  • A ranar Laraba 6 ga watan Satumba ne dai kotun ƙararrakin zaɓen ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da aka shigar kan Shugaba Tinubu
  • Bayan shafe sama da sa'o'i 10 ana dogon Turanci, kotun ta ce hujjojin Atiku da Peter Obi ba su da sahihanci
  • Sai dai Atiku Abubakar da Peter Obi ba su gamsu da hukuncin ba, inda suka sha alwashin daukaka kara

Kalabari, jihar Ribas - Fitacciyar mai yaɗa bushara da da'awar addinin Kiristanci, Naomi George, ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a rantsar da ɗan takarar jam'iyyar Labour a matsayin shugaban ƙasa.

Ta ce wahayin da aka yi ma ta ne ya nuna hakan, wanda lokacin cikarsa kawai ake jira, kasantuwar kowane wahayi yana da lokaci.

Ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, ranar Laraba, 7 ga watan Satumban da muke ciki.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi

Mai da'awa ta ce za a rantsar da Peter Obi nan ba da jimawa ba
Malamar da'awa Naomi George ta ce za a rantsar da Peter Obi matsayin shugaban ƙasa. Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naomi: Saura ƙiris a rantsar da Peter Obi

Naomi George ta bayyana cewa saura ƙiris wannan wahayin na ta na batun rantsar da Peter Obi ya tabbata.

Ta ce Shugaba Bola Tinubu zai sauka daga kan kujerarsa ya miƙawa Peter Obi nan ba da jimawa ba.

Ta ce a yanzu ba ta hangi ‘Sabuwar Najeriya’ da Peter Obi ya riƙa kira a yayin yaƙin neman zaɓensa ba, inda ta bayyana cewa koma baya da wahalhalu, da ɓacin rai kawai take hangowa.

Yahaya Bello ya shawarci Atiku da Obi su guji asarar kudi

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan shawarar da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bai wa 'yan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi bi da bi.

Kara karanta wannan

To Fa: Miji Ya Tsorata, Ya Garzaya Kotu Yayin Da Matarsa Ta Yi Barazanar Sake Yi Masa Kaciya a Kano

Ya ce kamata ya yi Atiku da Obi su hakura da batun daukaka ƙara a kotun ƙoli, domin kuwa ba za su yi nasara akan Shugaba Bola Tinubu ba.

Ya ƙara da cewa ƙoƙarin daukaka karar da suke yi ba shi da wani alfanu, domin kuwa za su yi asarar kuɗi ne kawai.

Wike ya ce masoyan Obi ba su san siyasa ba

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shaguɓen da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi wa Peter Obi da magoya bayansa bayan hukuncin kotun zaɓe.

Wike ya ce tuntuni shi dama ya san da cewa Peter Obi ba zai iya lashe zaɓen ba, sannan kuma masoyansa ba su san yadda siyasar Najeriya ke tafiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng