Atiku da Peter Obi Sun Lashi Takobin Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli

Atiku da Peter Obi Sun Lashi Takobin Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli

  • Atiku Abubakar da Peter Obi sun yi fatali da hukuncin Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban ƙasa, zasu ɗaukaka ƙara
  • Jim kaɗan bayan yanke hukunci ranar Laraba, Lauyoyin Atiku da Peter Obi sun tabbatar da cewa zasu kalubalanci hukuncin a Kotun Ƙoli
  • Kotun zaɓe mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bayan ta kori kararrakin da aka shigar gabanta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da takwaransa na Labour Party, Peter Obi, sun bayyana cewa zasu ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Kotun zaɓe ta yanke.

Kotun suraron ƙorafe-korafen zaben shugaban kasa, ranar Laraba, ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan korar kararrakin Atiku, Obi da APM, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: An Bayyana Wani Muhimmin Dalili Da Zai Sanya Shugaba Tinubu Ya Cigaba Da Nasara Akan Atiku Da Peter Obi

Atiku Abubakar tare da Peter Obi.
Atiku da Peter Obi Sun Lashi Takobin Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli Hoto: thecable
Asali: UGC

Da yake hira da manema labarai jin kaɗan bayan kammala zaman Kotun wanda ya shafe awanni kusan 13, Lauyan Obi da LP, Livy Uzoukwu, ya ce zasu ɗaukaka ƙara zuwa gaba.

"Waɗanda nake wa aiki ba su gamsu da wannan hukuncin da Kotu ta yanke ba, na samu umarnin cewa mu ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin. Muna sa ran zuwa gobe za a bamu kwafin hukuncin."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan Atiku ya tabbatar da cewa zasu tafi Kotun koli

A nasa ɓangaren, lauyan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Chris Uche, ya ce Kotu ta yanke hukunci amma ba ta musu adalci ba, kamar yadda Punch ta rahoto.

A kalamansa, Lauyan Atiku ya ce:

"Kotu ta bayyana hukuncin da ta yanke amma a zahirin gaskiya mu ba a mana adalci ba, abun farin cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya ba mu 'yancin ɗaukaka ƙara."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Taya Shugaba Tinubu Murnar Samun Nasara a Kotu? Gaskiya Ta Bayyana

"Wannan ita ce Kotun farko, muna da ikon zuwa gaba Kotun koli. Fafutukar nan da kuke gani ba ta wanda muke karewa (Atiku) kaɗai bace, har da kwansutushin, doka da Demokuraɗiyya."
“Muna da umarni daga wanda muke karewa cewa mu tafi kotun koli. Saboda haka, mun nemi bayanan hukuncin da aka yanke."

Hadamar Atiku Ce Ta Jawa Jam'iyyar PDP Rashin Nasara, VON DG

A wani rahoton na daban Shugaban VON ya bayyana babban dalilin da ya sa PDP ta sha kashi a babban zaben 2023 da ya gabata.

Osita Okechukwu ya ce Atiku yana da haɗama da kwaɗayin mulki domin da ya mara wa ɗan kudu baya da wataƙila yanzu wani zancen ake daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel