Fasto Kingsley Ya Bayyana Yadda Peter Obi Zai Kwace Mulki A Hannun Tinubu A Kotu

Fasto Kingsley Ya Bayyana Yadda Peter Obi Zai Kwace Mulki A Hannun Tinubu A Kotu

  • Kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta sanar da ranar Laraba 6 ga watan Satumba a matsayin ranar yanke hukunci
  • Wannan sanarwa ta yi dai-dai da sanarwar da wani mashahurin Fasto ya yi inda ya bayyana abin da zai faru tsakanin ‘yan takarar
  • Fasto Kingsley Okwuwe ya ce ubangij ya fada masa zai turo wani mutum mai siffar Cyrus da zai karbi mulki ya bai wa Peter Obi

FCT, Abuja – Yayin aka saka ranar yanke hukuncin na zaben shugaban kasa, wani shahararren Fasto ya bayyana abin da zai faru, Legit.ng ta tattaro.

Fasto Kingsley Okwuwe na Revival and Restoration Mission ya ce dan takarar shugaban kasa a jam’iyar Labour, Peter Obi zai karbi mulkin da aka kwace masa.

Fasto ya bayyana yadda Peter Obi zai kwace mulki a ranar Laraba a kotu
Fasto Kingsley Ya Yi Bayanin Yadda Peter Obi Zai Yi Nasara A Kotu. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi.
Asali: Facebook

Meye Faston ya ce kan Peter Obi?

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Magana, Ya Haska ‘Barnar’ da Gwamnatin Buhari Tayi a Shekaru 8

Faston ya bayyana haka ne a yau Litinin 4 ga watan Satumba a sahfinsa na YouTube inda ya ce ubangiji zai turo wani don kwace mulkin a hannun Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tabbas sabuwar Najeriya na nan tafe wanda shi ne ainihin abin da Peter Obi ke tallata kanshi yayin yakin neman zabe.

Ya ce:

“Ubangiji ya fada min, kuma na gani a mafarki yayin da ya tabbatar min da maganar.
“Cyrus zai zo, wannan Cyrus da zai zo wanda dan Adam ne amma ba Peter Obi ba, Cyrus zai kasance kamar John da ya samar da hanya ga Almasihu.”

Yaushe ne hukunci tsakanin Atiku, Peter Obi da Tinubu?

Ya kara da cewa:

“Wadanda su ka hada baki aka kwace mulkin Obi dukkansu sun shiga uku.
“Sun riga sun shiga teku mai launin ja, kuma kwalekwale zai nitse da su a cikin tekun.”

Kara karanta wannan

Tsabagen Kiyayya Ya Jawo Mawaki Ya na Kiran Sojoji Su yi wa Tinubu Juyin Mulki

Idan ba a mantaba kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci.

Shari’ar da ake yi tsakanin Shugaba Tinubu na APC da kuma Atiku Abubakar daga jam’iyyar PDP sai kuma Peter Obi daga jam’iyyar Labour na daf da karewa.

Kotun a tabbatar da yanke hukuncin na karshe a ranar Laraba 6 ga watan Satumba a Abuja.

Fasto Elijah Ya Aike Da Muhimmin Gargadi Ga Peter Obi Kan Shari'ar Zabe

A wani labarin, David Elijah, shugaban cocin Glorious Mount of Possibility Church, ya gargadi Peter Obi.

Fasto David ya gargadi dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour (LP) da ya yi taka tsan-tsan da wasu na kusa da shi da masu goyon bayansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel