Jigo Ya Tsere Ya Bar Su Kwankwaso a NNPP, Ya Ce Rikicin Gidan Jam’iyyarsu da Yawa

Jigo Ya Tsere Ya Bar Su Kwankwaso a NNPP, Ya Ce Rikicin Gidan Jam’iyyarsu da Yawa

  • Bem Angwe ya fitar da sanarwa na musamman cewa ya hakura da zama a jam’iyyar adawa ta NNPP
  • Farfesan ya ba komai ya jawo ya dauki wannan mataki ba illa sabanin da ya addabi NNPP a yau
  • Tsohon mai ba jam’iyya shawara kan shari’ar na kasa ya zabi ya cigaba da koyarwa a makaranta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue - A halin yanzu Bem Angwe ya fita daga NNPP, jam’iyyar da aka taba jin shi ya na cika baki da cewa ita za ta yi galaba a zaben 2023.

The Cable ta ce Farfesa Bem Angwe ya fitar da jawabi a ranar Asabar, inda ya kafa hujja da ‘rikici’ da ‘hargitsi’ a matsayin dalilin barin NNPP.

Shugabannin NNPP sun samu labarin ficewar Angwe wanda asalinsa malamin makaranta ne kafin zama mai ba NNPP shawara kan shari’a.

Kara karanta wannan

Alamu Sun Nuna Abba Ya Karaya a Shari’ar Zaben Gwamna - Tsohon Hadimin Ganduje

NNPP a Benuwai
Kwankwaso ya na kamfe a NNPP a Benuwai Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Daga makaranta zuwa NNPP zuwa makaranta

Farfesan ya shaida cewa ya shirya komawa aji inda aka san shi da koyarwa, zai cigaba da bada gudumuwa wajen kare hakkin Bil adama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“La’akari da rikici mai ban takaici da hargitsin da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP a kowane mataki kuma kamar yadda tsarin mulkin NNPP na 2022 ya yi tanadi, A yau 26 ga Agusta), 2023, na janye zama ‘dan jam’iyyar NNPP.
Domin gudun rikici, na sanar da shugaban jam’iyya na reshen Mbatyu a karamar hukumar Gboko game da ficewa ta daga NNPP."

- Farfesa Bem Angwe

Angwe ya godwewa magoya bayan NNPP

A jawabin da ya fitar ranar Asabar, ‘dan takaran gwamnan na Benuwai a 2023 ya yi godiya ga ‘yan NNPP na mazabarsa da magoya bayansa.

Blueprint ta ce Angwe ya yi godiya ga wadanda su ka mara masa baya da ya ke neman takarar da Hyacinth Alia ya yi nasara a APC.

Kara karanta wannan

Hanzari ba gudu ba: Shehu Sani ya shawarci Wike kan yadda ya rabi APC, ya nemi ya bar PDP

Ina labarin nasarar jam'iyyar NNPP?

Watanni bakwai da su ka wuce aka ji Farfesan ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyya mai alamar kayan dadi har ya hango nasara.

A lokacin da aka rantsar da Augustin Ogbuji ya zama shugaban yakin zabe, ‘dan takaran ya ce NNPP za tayi galaba kan manyan jam'iyyu.

APC ta karbe kujerar LP

Kujerun da APC ta ke da shi a majalisar wakilan tarayya sun karu da aka ji labari an tsige ‘dan majalisar jam’iyyar LP mai wakiltar mazabar Ojo.

Duk tulin kuri'un da LP ta samu a a zaben 'dan majalisar wakilan sun tashi a banza a zaben 2023, kotun sauraron karar 2023 ta ba APC nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng