Wike Na Hawa Motar Miliyan 300 Wacce Harsashi Bai Ratsa Ta? Ministan Abuja Ya Fayyace Gaskiya

Wike Na Hawa Motar Miliyan 300 Wacce Harsashi Bai Ratsa Ta? Ministan Abuja Ya Fayyace Gaskiya

  • Ministan Abuja Nyesom Wike ya yi martani ga rahotannin cewa ya siya motar miliyan 300 da kama aikinsa
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa motar ba wanda harsashi bai ratsawa bane kamar yadda aka rahoto, illa motar SUV ce da aka saba gani
  • Ministan ya kuma bukaci kafofin watsa labarai da su dunga yin abun da ya dace ta hanyar tabbatar da bayani daga majiya mai tushe kafin wallafa ta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi martani ga rahotannin soshiyal midiya cewa ya siya motar miliyan 300 wacce harsashi baya ratsa ta a yayin da ya kama aiki.

Wike ya karyata rahotannin sannan ya kalubalanci yan jarida da su taba motar domin su tabbatar da ko mota ce wacce harsashi bai ratsawa da gaske ko akasin haka, rahoton AIT.

Kara karanta wannan

Albashi Da Allawus Din Ministocin Tinubu Ya Bayyana, Za Su Lakume Biliyan 8.6

Wike ya ce bai siya motar miliyan 300 ba
Wike Na Hawa Motar Miliyan 300 Wacce Harsashi Bai Ratsa Ta? Ministan Abuja Ya Fayyace Gaskiya Hoto: Viable Tv, The Punch
Asali: Facebook

Bayan ziyarar aiki da ya kai tashar jirgin kasan Abuja, ministan ya ce:

"Yanzu za mu tafi ofis don samun rahoton kai tsaye daga kowani sashi, amma na ga abun da ke faruwa a soshiyal midiya; yadda ke (sakatariyar dindindin na hukumar birnin tarayya) kika siya motar miliyan 300 da harsashi bai ratsa ta da nake amfani da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka, ina so ku je ku buga hannunku a chan (jikin motar) sannan ku gani ko motar da harsashi bai ratsawa ne. Cike da girmamawa, ya kamata mutane su yi taka tsan-tsan kada su bata sauran mutane.
"Da na zo, sakatariyar dindindin ta ce sun tanadar mana da mota, kuma motar da muka yi amfani da ita itace wannan. Ban amince a siya kowace mota ba kuma ban yi amfani da motar aiki da harsashi bai ratsata ba. Ko ina da motoci a matsayin gwamna? Eh, a matsayin gwamna, me kuke tsammanin zan mallaka? Amma, bana amfani da motar da harsashi bai ratsata a matsayin ministan Abuja, don haka mu kawo rahoton abun da yake daidai, sannan kada mu bata kanmu. Ina so ku kalli inda ake da tuta, sannan ku ga ko motar da harsashi bai ratsawa ne."

Kara karanta wannan

Wike Ya Jero Mutanen Da Zai Cusa Kafar Wando Daya Da Su Bayan Zama Minista

Kalli bidiyon Wike yayin da ya ce bai siya motar miliyan 300 ba

Karamar ministar Abuja, Dr Mariya Mahmoud da sakataren dindindin na babban birnin tarayyam Olusade Adesola ne suka yi wa Wike rakiya zuwa tashar jirgin kasan.

Wike ya bai wa yan kwangila wata takwas su kammala aikin layin dogo na Abuja

A gefe guda, mun ji cewa a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya bayar da sabon umurni game da aikin layin dogo.

Wike wanda ya nuna bacin rai a kan halin da layin dogon na Abuja ke ciki, ya umurci sakataren dindindin da ya biya kamfanin China da ke aikin cikakken kudi domin a kammala aikin gyaran hanyar jirgin kasan cikin wata takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng