Wike Ya Ce Masu Sayar Da Masara Na Janyo Matsalar Tsaro a Birnin Tarayya Abuja

Wike Ya Ce Masu Sayar Da Masara Na Janyo Matsalar Tsaro a Birnin Tarayya Abuja

  • Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya haramta kasuwancin da ake yi kan titunan cikin unguwanni
  • Daga cikin irin waɗanda ya haramta akwai sana'ar sayar da masara a titunan unguwannin na Abuja
  • Wike ya ce masu aikata miyagun laifuka suna fakewa wajen masu sayar da masara suna lura da inda za su yi ta'addanci

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, Nyesom Wike, ya ce masu saide-saide a cikin unguwanni, cikinsu har da masu sayar da masara ne ke janyo matsalar tsaro a cikin birnin.

Wike ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da da ma'aikatan gudanarwa da na ci gaban FCT, inda ya buƙaci kowanensu ya maida hankali wajen yin abinda ya dace.

Ministan Birnin Tarayya (FCT) Abuja ya ba da sabuwar sanarwa
Wike ya ce masu sayar da masara na kawo matsalar tsaro a Abuja. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Wike ya ce masu sayar da masara na tara masu aikata laifuka

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari’a Ta Bai Wa Magidanci Masauki a Gidan Yari Kan Lakadawa Tsohuwar Matarsa Duka

Wike ya ce ba zai lamunci ci gaba da barin mutane suna saide-saide barkatai a kan titunan cikin Abuja ba, a domin haka ya haramta duk wani nau'i na irin wannan kasuwancin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa masu sayar da masara suna tara masu aikata laifuka, waɗanda ke fakewa da sunan sayan masara suna lura da inda za su yi ta'addanci.

Haka nan kuma ya ƙara da cewa masu sana'ar masarar na ɓata titunan cikin birnin da ɓawo, wanda yakan ƙara gurɓata muhalli kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wike ya ce zai mayar da Abuja yadda take a baya

Wike ya kuma bayyana cewa zai yi ƙoƙarin mayar da birnin na tarayya yadda aka tsaro shi tun asali, inda ya ba da tabbacin cewa za su rushe duk ginin da aka yi ba bisa ƙa'ida ba. kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Wani Dan Bindiga Ya Sheƙe Mutane 3 a Wata Fitacciyar Mashayar Giya a Amurka

Ya kuma tabbatar da cewa zai tsaftace Abuja, inda ya ba da umarnin a fara aiki tsaftace birnin, tare da shelanta cewa zai iya tuntubar duk wani ma'aikacin tsaftar muhalli a kowane lokaci.

Wike ya kuma ba da tabbacin cewa zai yi ƙoƙarin gyara wutar lantarki ta yadda za a samu wadataccen haske a cikin birnin.

Wike ya bukaci ma'aikatan da ke ƙarƙashinsa su zage damtse

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan zaburar da ma'aikatan ma'aikatar kula da Babban Birnin Tarayya Abuja da Minista Nyesom Wike ya yi.

Wike ya ce dole ne kowane ma'aikaci ya zage damtse wajen yin abinda ya kamata, inda ya ƙara da cewa duk wanda ba shirin aiki ya zo ba to ya nemi canjin wurin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel