Tsohon Gwamnan PDP Ya Fadi Ministoci 2 da Za Su Yi Kokari a Mulkin Bola Tinubu
- Samuel Ortom ya na ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai yi tumun dare a wajen zakulo ministocinsa ba
- A wani jawabi da ya fitar ta bakin Terver Akase, tsohon gwamnan ya jinjinawa wasu ministocin kasar
- Ortom ya ce Wike zai kawowa Abuja cigaba, ya yabi cancantar Farfesa Joseph Utsev a ma’aikatar ruwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Benue - Tsohon gwamna a jihar Benuwai, Samuel Ortom ya ji dadin ganin yadda Nyesom Wike da Joseph Utsev su ka zama ministocin tarayya.
Samuel Ortom wanda ya na cikin ‘yan kungiyar G5 a jam’iyyar PDP ya yi farin ciki da mukaman da aka ba Farfesa Joseph Utsev da Nyesom Wike.
Dazu The Sun ta rahoto ‘dan siyasar ya na mai bayanin alakarsa da wadannan mutum biyu da Bola Tinubu ya rantsar a matsayin ministocinsa.
Samuel Ortom a kan Wike, Utsev
Ortom ya bayyana tsohon gwamnan na Ribas da yanzu yake rike da ma’aikatar birnin tarayya da wanda ya sani a matsayin aboki a tafiyar siyasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A game da Farfesa Utsev wanda ya zama ministan ruwa da tsabta, Mista Ortom ya ce ya yi aiki da shi a lokacin da ya ke kan kujerar gwamna a Makurdi.
Jawabin Terver Akase
Vanguard ta ce bayanin ya fito ta ofishin mai magana da yawun bakin gwamnan, Terver Akase, ya na mai yabawa zabin da shugaban Najeriya ya yi.
Terver Akase ya kara da cewa Wike zai kawo cigaban da ake nema a birnin tarayya na Abuja, har an ji ya soma bayanin yadda zai jagoranci ma'aikatar.
Shi kuwa Joseph Utsev, ya rike kwamishinan harkokin ruwa da muhalli a Benuwai, saboda haka ya ke ganin ya cancani ma’aikatar da aka damka masa.
Ortom wanda shi kan shi ya yi minista a gwamnatin Goodluck Jonathan kafin ya nemi takara a gida, ya ce wadannan mutane ba za su bada kunya ba.
Baya ga su, akwai sauran ministoci fiye da 40 da su ka shiga ofis da aka rantsar da su a makon nan. Wike ne kawai fitaccen ‘dan jam’iyyar PDP a cikinsu.
Ina 'Yan G5 su ka shige?
A lokacin zaben shugaban kasa na 2023, sabon ministan na Abuja ya jagoranci wasu jiga-jigan ‘yan PDP, su ka yaki ‘dan takaransu watau Atiku Abubakar.
Da farko kun ji rahoto ya zo cewa kusan duka 'yan G5 ba su ce uffan ba yayin da labari ya zo cewa Wike ya zama minista a gwamnatin APC mai-ci.
Asali: Legit.ng