Nadin Ministoci: Ba Za Mu Goyi Bayan Wanda El-Rufai Ya Bada Sunan Shi ba – Jigon APC
- Nasir El-Rufai ya tsokano rikici a APC da ya bada sunan wanda zai maye gurbinsa a cikin Ministoci
- A matsayinsa na cikakken ‘dan jam’iyya mai-ci, Muhammadu Murtala zai yaki tsohon jagoransa
- ‘Dan siyasar ya na ganin bai dace El-Rufai ya tsaida wanda yake so ba tare da an zauna da ‘yan APC ba
Kaduna - Muhammadu Murtala ya na cikin jagorori a jam’iyyar APC a jihar Kaduna, ya tattauna da ‘yan jarida game da siyasarsu ta cikin gida.
A wata hira da Daily Trust tayi da shi, Muhammadu Murtala ya yi magana game da wanda ake so ya wakilci Kaduna a majalisar ministoci ta FEC.
Ana tunanin bada sunan Jafar Sani Ibrahim da Malam Nasir El-Rufai ya yi, ya jawo sabani tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen jihar Kaduna.
Sai an zauna da 'yan APC na Kaduna
Shi Muhammadu Murtala ya na ganin idan har akwai rashin jituwa a kan kujerar minista daga Kaduna, tsohon gwamnan ne ya jawo rigimar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar ya zargi Nasir El-Rufai da daukar mataki shi kadai ba tare da ya tuntubi sauran ‘yan jam’iyya ba a yayin da aka gagara tantance shi.
"El-Rufai bai tuntube mu ba"
Idan har akwai sabani a cikin jam’iyyar, watakila saboda yadda El-Rufai ya tafi ne da kuma matakin da ya dauka shi kadai na zakulo wani.
Ya tuntubi masu ruwa da tsaki na jam’iyya kafin bada sunan wanda zai canje shi a minista?
Shin ya tuntube mu? Ya shigo jam’iyyarmu, amma babu wanda ya tuntube ni. Sannan ba a tuntubi da-dama daga cikinmu (‘ya ‘yan APC) ba.
Bai sha’awa domin ba a amince da shi ba, kuma sai ya jawo wani a madadinsa. Menene bambancinsa da wanda ya bada, duk daya su ke.
- Muhammad Murtala
A tattaunawa da jaridar, ‘dan siyasar ya nuna ba za su yarda Shugaba Bola Tinubu ya amince da wanda Malam El-Rufai ya kai masa sunansa ba.
Girman ka, girman akwatinka
Kafin a yanke shawara, jigon ya ce sai an zauna da su kamar yadda aka yi lokacin kamfe, sai a dauki wanda ya fi ba jam’iyya gudumuwa a zabe.
"Bai dacewa saboda sanayya a bada sunan wani a mukamin da ke bukatar masu ruwa da tsaki. Zan yi yaki da wannan, mu na da cewa a jam’iyya."
- Muhammad Murtala
Rusau a garin Abuja
Ana da labari kamar yadda Nasir El-Rufai ya yi a Abuja, Nyesom Wike zai yi karin kumallo da makiyaya, ‘Yan Acaba da asu gidaje a birnin tarayya.
Minista ya ce kasuwanni sun yi yawa, haka shanu da 'yan acaba. A cewarsa ba za ta yiwu a rika cin karo da shanu da awaki a kan hanyar Aso Rock ba.
Asali: Legit.ng