PDP Ta Gaji, Za Ta Hukunta Wike da Sauran Gwamnonin da Su ka Yi wa Tinubu Aiki
- Shugabannin jam’iyyar PDP ba za su cigaba da zama tare da wadanda su ka yake ta a 2023 ba
- Wasu jagororin adawa sun yi watsi da takarar Atiku Abubakar, su ka taimaki Bola Tinubu a zabe
- Nan gaba kadan shugabannin PDP za su hukunta ‘ya ‘yanta da aka samu da laifin shirya zagon-kasa
Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta na kokarin ganin kawo karshen barakar da aka samu tun bayan zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasan 2023.
Wani rahoto na Daily Trust ya ce babbar jam’iyyar adawar za ta ladabtar da tsohon Gwamna Nyesom Wike da kuma sauran ‘yan tafiyarsa ta G5 a PDP.
Wike da mutanensa da su ka kira kansu ‘Integrity Group’, sun ki goyon bayan Atiku Abubakar a zaben 2023, abin bai tsaya nan ba, sun taimakawa APC.
Tun bayan zaben babu abin da aka yi wa ‘yan tawayen illa tura Samuel Ortom zuwa gaban kwamiti, sannan aka dakatar da Ayo Fayose daga jam’iyya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shi kuwa Wike wanda ya dage sai da aka yi waje da Iyorchia Ayu daga kujerar shugaban NWC, ya kalubalanci NEC ta dakatar da shi daga PDP.
Wani mataki PDP za ta dauka a kan G5>
Rahoton ya ce an samu sabani tsakanin shugabannin jam’iyya game da matakin da ya fi dacewa a dauka game da wadanda su ka yaki Atiku Abubakar.
Tun tuni aka shigar da kara a hana shugabanni da uwar jam’iyya a kan dakatar da mutanen Wike. Wasu su na ganin babu dalilin a fatattaki G5.
A karshen wani taro da kungiyar gwamnonin jihohin PDP su ka yi kwanaki, sun shaida cewa ba za su yarda da zagon kasan daga ‘ya ‘yan jam’iyya ba.
Shugaban kungiyar, Gwamna Bala Mohammed ya ce an amince a hukunta maciya-amana, ‘yan G5 su na cikin wadanda su ka halarci zaman da aka yi.
Wike zai koma Jam'iyyar APC daga PDP?
Zaben shi a matsayin minista da rantsar da shi da Bola Tinubu zai yi a ranar Litinin ya canza lamarin bayan Wike ya ziyarci sabon shugaban APC.
A makon nan aka ji tsohon Gwamnan ya je gidan Abdullahi Ganduje. Wani matashin ‘dan APC a Kaduna ya fada mana da alamun Wike zai bar PDP.
Daga baya an ji tsohon Gwamnan Kano ya na nuna 'yan adawa za su shigo APC mai-ci.
Asali: Legit.ng