Wike Ya Sake Nasara Akan PDP, Wata Babbar Kotu Ta Aikewa Jam'iyyar Sabon Umarni

Wike Ya Sake Nasara Akan PDP, Wata Babbar Kotu Ta Aikewa Jam'iyyar Sabon Umarni

  • Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya sake samun nasara akan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP)
  • Wata babbar kotun tarayya ta hana jam'iyyar PDP dakatar da ko korar gwamnan daga jam'iyyar
  • Gwamna Wike ya daɗe yana takun saƙa da jam'iyyar PDP tun bayan da ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasan a inuwar PDP

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a birnin tarayya Abuja, ta haramtawa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga dakatarwa ko korar gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike daga jam'iyyar.

Kotun ta kuma hana jam'iyyar PDP ɗaukar irin wannan matakin akan mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar na jihar Rivers, bisa zargin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Kotu ta hana PDP dakatar da Wike
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Da yake zartar da hukuncinsa, mai shari'a Inyang Ekwo, ya ce ya gamsu da tsoron da Wike da sauran ƴaƴan jam'iyyar suke yi, sannan dakatar da su ko korar siu zai sanya a take musu haƙƙin su na ƴancin ƙulla alaƙar ƙawance da wasu.

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Jam'iyyar APC Ta Kori Babban Sanata Mai Ci a Jihar Arewa, Ta Bayar Da Dalilai

A saboda haka alƙalin sai ya bayyana cewa, hurumin kotun ne ta samar wa da mutanen da suka gabatar da wasu dalilai da za su sanya a take musu haƙƙin su mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aƙalin ya bayyana cewa ba za a iya dakatar da ƴaƴan jam'iyya haka nan kawai ba, ba tare da an bi kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba, cewar rahoton Leadership.

Wike, da sauran wasu gwamnonin jam'iyyar PDP gudu huɗu, waɗanda aka fi sani da G5, sun kwarewa jam'iyyar zani a kasuwa inda suka riƙa yin kamfen ɗin kada a zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasar jam'iyyar Alhaji Atiku Abubakar.

An Bankado Wani Laifin Tinubu Da Ka Iya Hana a Rantsar Da Shi

A wani labarin na daban kuma, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na fuskantar zargin yin rantsuwa a bisa ƙarya.

Kara karanta wannan

Badakalar Kudi: Rarara Ya Nemi Kotun Shari'ar Musulinci Tayi Watsi Da Karar Da Ake Masa, Ya Bayar Da Dalilin Sa

Ana zargin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da ɓoƴe cewa shi ɗan ƙasa biyu ne, inda aka ce yana da fasfo ɗin zama ɗan ƙasar Guinea Conakry.

Wata ƙungiyar magoya bayan Peter Obi na jam'iyyar Labour Party, ta yi kira ga Tinubu da ya fito ya wanke kan shi kan zargin da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel