Babban Jami'in Gwamnati Ya Bayyana Ma'aikatar Da Za a Tura El-Rufai
- Har yanzu Nasir El-Rufai na iya zama minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Duk da majalisar Dattawan Najeriya ba ta tabbatar El-Rufai ba, har yanzu zai iya bin sahun ministoci 45 da aka ayyana
- Wani babban jami'i a ma'aikatar muhalli ta ƙasa, ya shaidawa Legit.ng cewa gurbin ministan muhalli an ajiye shi ne domin El-Rufai
FCT Abuja - An bayyana cewa Tinubu ya riga da ya sanya sunan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin wanda zai naɗa ministan muhalli a gwamnatinsa.
Wani babban jami'i a ma'aikatar muhalli ta tarayya, ya shaidawa Legit.ng cewa an ajiye wannan gurbin ne musamman domin El-Rufai a yayin da ake jiran Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi.
An warewa El-Rufai ma'aikatar muhalli
El-Rufai daga Kaduna, Stella Okotete daga Delta da kuma Abubakar Danladi daga jihar Taraba ne mutane ukun da har yanzu ake gudanar da bincike a kansu, wanda hakan ya hana a tabbatar da su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kasantuwar dukkansu mambobin jam'iyyar APC mai mulki ne, har yanzu za su iya zama ministoci idan Majalisar Dattawan ta tabbatar da su.
A cikin mutane 45 da Tinubu ya sanar da ma'aikatun da aka tura su, ya bayyana ƙaramin minista na muhalli, inda bai bayyana sunan babban ministan ba, wanda jami'in ya shaidawa Legit.ng cewa El-Rufai aka warewa ita.
Tinubu zai yi koyi da Buhari, zai riƙe ministan mai
A baya Legit.ng ta kawo rahoto cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai yi koyi da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a tsarin rabon muƙamansa.
Kamar yadda Buhari ya riƙe muƙamin ministan man fetur na wa'adin shekaru takwas a zamaninsa, Shugaba Bola Tinubu ma ya nuna alamar ɗaukar hanya.
A cikin ministoci 45 da Tinubu ya ayyana ma'aikatun da ya turasu a ranar Larabar da ta gabata, ya zaɓi Heineken Lokpobiri a matsayin ƙaramin ministan man fetur kamar yadda The Cable ta wallafa.
El-Rufai ya hakura da zama minista a gwamnatin Tinubu
Legit.ng a baya ta kawo rahoton cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nuna cewa baya sha'awar riƙe muƙami a gwamnatin Bola Tinubu.
Ya bayyana hakan ne biyo bayan ƙin tabbatar da shi da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi a yayin da aka tabbatar da mutane 45 da Tinubu zai naɗa ministoci.
Asali: Legit.ng