Atiku Abubakar ya Ziyarci Rabiu Kwankwaso Watanni 5 Bayan Zaben Shugaban Kasa
- Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban Najeriya a gidansa
- Ziyarar ta bar jama’a a cikin duhu, har yanzu babu wanda ya san abin da ‘yan siyasar su ka tattauna
- Kwankwaso da Wazirin Adamawa sun gwabza wajen neman kujerar shugaban kasa a PDP da NNPP
Abuja - A yammacin Talata, 15 ga watan Agusta 2023, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi ziyarar da ta bada mamaki.
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da haka a shafinsa.
Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar GCFR ya taka da kafafunsa ya ziyarci jagoran adawa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.
Maganar da Kwankwaso ya yi
‘Yan siyasar biyu duk sun nemi takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023, amma ba su yi nasara ba, Bola Ahmed Tinubu ya yi galaba a kan su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Na yi farin cikin tarbar ‘danuwa na, Alhaji tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a gida na da yamman nan.
Na godewa Waziri da wannan ziyarar 'yanuwantaka.”
- Rabiu Musa Kwankwaso
Magoya baya su na ta maganganu
A shafin wani babban masoyin Kwankwaso a Twitter, @Babarh, an ga bidiyon wannan haduwa wanda jama’a su ke ta magana a game da ita.
Bisa dukkan alamu, Atiku Abubakar ya dauki tawagarsa ne zuwa gidan tsohon Gwamnan na Kano wanda ya zo na hudu a zaben da aka yi bana.
Tinubu bai tafi da Kwankwaso ba
Zuwa yanzu babu wanda ya san abin da ‘yan siyasar su ka tattauna, hakan na zuwa ne bayan tunanin Kwankwaso zai yi aiki da gwamnatin APC.
Da aka tashi fitar da ministoci, ba a ga sunan jagoran na NNPP a wadanda aka zaba ba. Ana tunanin hakan bai rasa nasaba da halin siyasar Kano.
An Sha Shagalin Bikin Dan Majalisar Kaduna, Bello El-Rufai Da Tsaleliyar Amaryarsa, Hotunan Sun Dauki Hankali
Me Atiku ya tattauna da Kwankwaso?
Akwai masu rade-radin Atiku ya ziyarci Kwankwaso ne saboda tunanin kotu za ta umarci a maimaita, wasu kuma sun ce shirin 2027 ne ake yi.
Siyasa babu abokin gaba na har abada, masu bibiyar lamuran siyasa su na ganin Waziri ya na so ya hada-kai da su Kwankwaso ne tun da wuri
...Wike ya je wajen Ganduje
Ku na da labari Abdullahi Umar Ganduje da Nyesom Wike sun sa labule a wata ziyara da ta ja hankalin kowa, an fara tunanin 'dan siyasar zai bar PDP.
Tsohon Gwamnan Ribas ya taya Ganduje murna ganin ya karbi shugabancin APC inda kwanan nan Wike zai zama Minista a gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng