Sanatan Arewa Ya Yi Caccaka, Sannan Ya Fallasa Kudin Hutun da Ake Rabawa Sanatoci

Sanatan Arewa Ya Yi Caccaka, Sannan Ya Fallasa Kudin Hutun da Ake Rabawa Sanatoci

  • Bulaliyar Majalisa ya bulale Godswill Akpabio, akwai yiwuwar Sanatoci su hukunta Shugabansu
  • Sanata Muhammad Ali Ndume bai ji dadin yadda aka shaidawa duniya cewa an biya su kudin hutu ba
  • ‘Dan majalisar ya ce wannan al’ada ce a majalisar tarayya tun 1999, ba a kan su aka fara biyan kudin ba

Abuja - Muhammad Ali Ndume wanda shi ne bulaliyar majalisar dattawa, ya ce babu laifi idan an biya Sanatoci N2m a matsayin kudin zuwa hutu.

Da aka yi hira da shi a BBC Hausa a ranar Asabar, Sanata Muhammad Ali Ndume ya nuna raba masu N218m da aka yi ba wani kayan gabas ba ne.

Kalaman da Godswill Akpabio ya yi sun jawo surutu a Najeriya, har yanzu maganar ba ta lafa ba. Hakan na zuwa ne bayan tantance ministocu.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Sanatoci a Majalisa
Wasu Sanatoci a Majalisar Dattawa Hoto: The Senate President - Nigeria
Asali: Facebook

Kudin halal ko na haram?

A hutun da za su yi daga makon jiya zuwa karshen Satumba, Premium Times ta ce an batar da fiye da Naira miliyan 200 a kan ‘yan majalisar dattawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana zargin cewa hukumar RMAFC mai yake albashi ba ta san da zaman wadannan alawus ba, hakan ya na nufin a dokar kasa kudin ba su halatta ba.

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Kudancin jihar Borno a majalisar dattawa ya soki Godswill Akpabio a dalilin sanar da Duniya abin da sirrinsu ne.

Tashar Arise ta rahoto ‘dan siyasar ya na cewa biyansu kudin nan tamkar yadda sauran ma’aikata su ke karbar alawus ne idan sun dauki hutu a aiki.

Irinsu Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila sun tabbatar da cewa wannan kudi ya shigo asusunsu kamar yadda aka saba biyan 'yan majalisa tun 1999.

Kara karanta wannan

Katobarar Akpabio: Rahoto Ya Tabbatar Da Yawan Kudin Da Sanatoci Suka Raba a Matsayin Kudin Shakatawa Lokacin Hutu

Shugaban majalisa zai yabawa aya zaki

"Kowane Sanata ya karbi Naira miliyan biyu. Ina fadan wannan magana ne rai na a bace domin shi Godswill Akpabio ya jawo wannan hayanayi.
Ya yi kuskure a kalamansa, kuma nan ta ke na gargade shi cewa kalamansa ba su dacewa da jagora.
Asali ma mu na tunanin daukar kakkwaran mataki a kan shi idan ya cigaba da yin irin wadannan kalamai, ya na yi tamkar mu kananan yara ne."

- Muhammad Ali Ndume

Sanatoci sun roki Tinubu

Ministoci biyar kacal za a nada daga Kudu maso gabas, amma an warewa sauran yankuna kujeru da-dama, an ji labari hakan ya jawo maganganu.

Duka sanatocin jihohin yankin Ibo da ke majalisar dattawa sun ce adalcin da Bola Tinubu zai yi shi ne ya kara masu Ministoci ko da biyu su rage zafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng