Sanata Ndume ya fadi wanda ya fi kowa 'dacewa ya yi takarar Shugaban Najeriya a APC

Sanata Ndume ya fadi wanda ya fi kowa 'dacewa ya yi takarar Shugaban Najeriya a APC

  • Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce shi ne ya fadawa Hon. Rotimi Amaechi ya nemi shugaban kasa
  • Abin da ya sa Muhammad Ali Ndume ya ba Amaechi wannan shawara shi ne ya na ganin ya dace
  • ‘Dan majalisar ya ce Ministan ya fi irinsu Bola Tinubu da Yemi Osinbajo cancanta da tikitin APC

Abuja - Shugaban kwamitin harkar sojoji a majalisar dattawa, Muhammad Ali Ndume ya yi magana a game da takarar da Rotimi Amaechi yake yi.

Da aka yi hira da shi a shirin Politics Today a gidan talabijin na Channels, Muhammad Ali Ndume ya ce ya taka rawar gani wajen shigo da Ministan takara.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya na ganin Rotimi Amaechi zai yi kyau da shugaban Najeriya.

A ra’ayin Ndume, tsohon gwamnan na jihar Ribas yana da tarihi, da karfin da zai iya shugabantar Najeriya yadda ya kamata, sannan ya na da kaifin kwakwalwa.

Kara karanta wannan

Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

“Ina cikin wadanda suka nemi Amaechi ya fito takara. Ni na fara. Aiki na ne. Ina cikin wadanda suka fadawa Amaechi ya nemi shugaban kasa.”
“Dalili, ina jin cewa a irin wannan mawuyacin lokacin. mu na bukatar asalin ‘dan Najeriya ne ya yi takara, ba wanda za a duba yankin da ya fito ba.”
Rotimi Amaechi
Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Ba za a kawo wanda bai san kan aiki ba, wanda ba a shaida ya yi a baya ba, wanda bai da karfi da kuma basirar da zai yi takarar shugaban kasa.”

- Muhammad Ali Ndume

Amaechi ya fi kowa kyau a APC

Daily Trust ta bibiyi hirar da aka yi da ‘dan majalisar dattawa, ta rahoto shi yana cewa Ministan sufurin shi ne wanda ya fi kowa cancanta ya tsaya a jam'iyyarsu.

Kara karanta wannan

Buhari ya jawo an taso El-Rufai a gaba saboda kalaman da ya yi shekaru 9 da suka wuce

“A jam’iyyar APC, ina jin Rotimi Amaechi ne wanda ya fi kowa dacewa mu tsaida takara. Ba na so in ce ya fi duk sauran ‘yan takarar da ka lissafo.”
“Idan aka ce ya fi kowa, ba a nufin sauran ba su da kyau sosai . Idan ana da mutane da yawa da ke da kyau, za a dauki wanda ya fi ne, shi ne ya fi.”

- Muhammad Ali Ndume

Tun da Rotimi Amaechi ya ayyana niyyar takarar shugaban kasa a zaben 2023, kusan duk inda zai je tare ake ganinsa da Sanatan mai wakiltar kudancin jihar Borno.

Tinubu ya saki maganganu

A ranar Asabar da ta wuce ne aka ji labari babban 'dan siyasar nan, Asiwaju Bola Tinubu ya kaddamar da yakin neman zabensa ga matasan jam’iyyar APC.

Tinubu ya soki shugabannin da suka mulki kasar nan, ya yi ikirarin duk sun gaza cika alkawuran da suka yi, ya ce shi ba zai saba alkawari idan ya samu mulki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel