Yadda Nasir El-Rufai, Danladi da Okotete Suka Gamu Da Cikas Wajen Zama Ministoci

Yadda Nasir El-Rufai, Danladi da Okotete Suka Gamu Da Cikas Wajen Zama Ministoci

  • Nasir El-Rufai da Sani Danladi ba su cikin jerin wadanda ‘Yan Majalisa su ka yarda a nada Ministoci
  • Haka zalika babu sunan Misis Stella Okotete mai shekara 39 a jerin da aka fitar a yammacin Litinin
  • Jami’an tsaro su kan yi bincike a kan mutum, sannan su goyi bayan ya rike mukami ko akasin hakan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - An gama tantance sunayen wadanda aka gabatar domin su zama Ministoci, majalisar dattawa ta fitar da jerin mutanen da aka amince da su.

Ku na da labari babu sunayen Nasir El-Rufai, Abubakar Sani Danladi da Stella Okotete a jerin Ministocin da ‘Yan Majalisar tarayyan su ka amince.

BBC ta ce Shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya shaida cewa an karbi mutane 45 yayin da ake jiran sakamakon rahoton binciken ragowar ukun.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Na So Tinubu Ya Cire El-Rufai Cikin Ministocinsa, Sun Fadi Dalili

Ministoci
Nasir El-Rufai, Sani Abubakar Danladi da Stella Okoteteza su zama Ministoci? Hoto: Sen. Sani Abubakar Danladi, Nigeria Hall of Fame Records, Bashir El-Rufai
Asali: Facebook

El-Rufai bai samu shiga ba tukuna

An samu rahoton kwarewa da basirar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna ya nuna da ake yi masa tambayoyi a kan sha’anin wutar lantarki da ye je Majalisa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Sunday Karimi ya nemi ya kawo matsala, ya ce an samu wata kungiya da ta kawo korafi a kan abubuwan da El-Rufai ya yi da yake mulkin Kaduna.

Wasu kungiyoyi a kudancin Kaduna da mabiya shi’a da almajiran Dahiru Bauchin da aka samu matsala da su a 2020, su na cikin masu adawa da shi.

Kowa da huruminsa a dokar kasa

‘Dan siyasar ya so maida martani a majalisa, amma Akpabio ya tsaida shi, yake cewa jami’an tsaro ke da alhakin bincike, aikin majalisa shi ne yin tambayoyi.

Bisa al’ada, BBC ta ce jami’an DSS ne su ka yin bincike a kan mutum, sannan sai su gabatar da rahoto domin a nada shi a wani mukami ko akasin haka.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Majalisa Ba Ta Tabbatar da El-Rufa'i Ba, Ta Amince da Mutum 45

Sashe na 147 na kundin tsarin mulki ya ce manufar tantance mutum kafin ya rike mukami shi ne a taimakawa gwamnati wajen jawo kawo na kwarai.

Sanata Yemi Adaramodu wanda yake magana da yawun majalisa ya ce sun kammala aikinsu, shawara ta rage ga sauran bangarorin gwamnati.

Stella Okotete da Danladi

Tun da aka zabi Miss Stella Okotete a 2017 domin ta rike bankin NEXIM har zuwa yau ake ta yin korafi a kan ta, jami’an DSS ba su kai ga wanke ta ba.

Abubakar Sani Danladi tsohon Sanata yankin Arewacin Taraba ne da aka tsige shi a majalisa, baya ga haka ya taba zama Gwamn kuma ya sake takara.

Kafin zabe aka ji kotu ta wanke shi, ta halatta masa rike mukami a Najeriya, amma wannan bai sa hukumar DSS ta gama bincike har ta wanke shi ba.

Kafin 'yan majalisa su tafi hutu, sai da su ka amince da har wanda ya taba zaginsu.

Kara karanta wannan

Ministoci: Sanatoci sun Tantance Mutum 46, Jami’an Tsaro na Binciken Ragowar 2

El-Rufai ya amsa tambayoyi

Da ya bayyana a gaban majalisa, an ji yadda El-Rufai ya amsa tambayoyi kan lantarki, dai tun a lokacin aka fahimci akwai masu yaki da shi.

A baya, an taba samun wata kungiya da ta kai karar Okotete gaban CCB, ana zargin ‘yar siyasar da kin fadawa hukumar gaskiyar abin da ta mallaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng