Sanatoci Sun Tantance Mutum 45, An Dakatar da El-Rufai, Mutum 2 a Ministoci
- Sanatoci sun gama aiki a kan mutanen da aka gabatar masu domin ba su mukamin Ministoci a Najeriya
- Nasir El-Rufai da Abubakar Sani Danladi su na cikin wadanda ba a gamsu da su a Majalisar dattawa ba
- Sanatoci sun jingine Stella Erhuvwu Okotete wanda kafin yanzu ta rike shugabancin bankin NEXIM
FCT Abuja - Majalisar Dattawa ta kammala aikin tantance wadanda ake so su zama Ministocin tarayya, kuma ta gabatar da sunayen dukkansu.
Tashar NTA ta kawo jerin sunayen wadanda Sanatoci su ka amince da su, su ka gamsu Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada a gwamnatinsa.
Abin da ya ba mutane matukar mamaki shi ne yadda aka nemi sunayen wasu fitattun mutane a cikin wadanda aka gabatar, amma aka rasa.
El-Rufai da mutum 2
Majalisar dattawa ba ta amince da tsohon Gwamna Malam Nasir El-Rufai ba duk an tantance shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ya bayyana a gaban majalisa, an ji yadda El-Rufai ya amsa tambayoyi, sai dai tun a lokacin aka samu labari akwai korafin da aka shigar a kan shi.
A baya, an taba samun wata kungiya da ta kai karar Okotete gaban CCB, ana zargin ‘yar siyasar da kin fadawa hukumar gaskiyar abin da ta mallaka.
Shi kuwa Sanata Abubakar Sani Danladi an san cewa ana zargin kotu ta hana masa rike duk wani mukami, sai dai ‘dan siyasar ya musanya ikirarin.
Idan aka tafi a haka ba tare da ta canza zani ko an bada sunan wani dabam ba, jihar Kaduna za ta kasance ba ta da wakicli a majalisar zartawa ta FEC.
Wadanda aka tantance
1. ABUBAKAR KYARI
2. ABUBAKAR MOMOH
3. NYESOM WIKE
4. PROF. JOSEPH UTSEV
5. JOHN ENO
6. BELLO MOHAMMED
7. MOHAMMED BADARU ABUBAKAR
8. YUSUF MAITAMA TUGGAR
9. UJU KEN OHANEYE
10. OLUBUNMI TUNJI OJO
11. NKEIRUKA ONYEJEOCHA
12. BETTA EDU
13. IMAAN SULEIMAN
14. DAVID UMAHI
15. ADEBAYO OLAWALE EDUN
16. AHMAD DANGIWA
17. UCHE NNAJI
18. DELE ALAKE
19. WAHEED ADEBAYO ADELABU
20. MUHAMMAD IDRIS
21. PROF. ALI PATE
22. DR. DORIS UZOKA
23. LATEEF FAGBEMI (SAN)
24. EKPERIKPE EKPO
25. HANNATU MUSAWA
26. IBRAHIM GEIDAM
27. ALIYU SABI ABDULLAHI
28. HEINEKEN LOKPOBIRI
29. ALKALI AHMED SA'EED
30. DR. YUSUF TANKO SUNUNU
31. ATIKU BAGUDU
32. BELLO MATAWALLE
33. ADEGBOYEGA OYETOLA
34. SIMON LALONG
35. ABDULLAHI TIJJANI GWARZO
36. BOSUN TIJJANI
37. DR MARIYA MAHMOUD
38. DR ISIYAKA SALAKO
39. DR TUNJI ALAUSA
40. LOLA ADE JOHN
41. PROF. TAHIR MAMMAN
42. ZEPHANIAH JISSALO
43. UBA MAIGARI AHMADU
44. SHUAIBU ABUBAKAR AUDU
45. FESTUS KEYAMO (SAN)
Tinubu bai tsira ba
Rahoto ya zo kwanaki cewa wasu mutanen yankin Arewa sun soki Mai girma shugaban kasa da cewa bai zabo masu wakilai na kwarai ba.
Dama an ce ba a iyawa ‘Dan Adam domin ana tuhumar Tinubu da dauko kwararru daga jihohin Kudu da tattara tsohon Gwamnoni daga Arewa.
Asali: Legit.ng