Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da shari'ar hana Sani Contact takara

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da shari'ar hana Sani Contact takara

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa kotun daukaka kara dake zaune a Jalingo, birnin jihar Taraba ta yi watsi da hukuncin haramtawa dan takaran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, Alhaji Sani Abubakar Danladi, takarar zabe.

A jiya mun kawo muku rahoton cewa wata babban kotun tarayya dake zaune a Jalingo, babbar birnin jihar Taraba a ranar Laraba ta janye dan takaran gwamnan jihar Taraba karkashin jam'iyyar Sani Abubakar Danladi, daga takarar zaben ranar Asabar.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bisa ga zargin karyan yawan shekarun da dan takaran yayi a takardun da ya aikawa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC.

Ku saurari cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng