Adamu Bai Yi Murabus Don Gano Kotu Ta Rushe Zaben Tinubu Ba, Binciken Gaskiya Ya Bayyana

Adamu Bai Yi Murabus Don Gano Kotu Ta Rushe Zaben Tinubu Ba, Binciken Gaskiya Ya Bayyana

  • Wasu faya-fayen bidiyo da aka yada a Facebook sun yi ikirarin cewa Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa saboda rashin tabbas din shari'ar Tinubu da ake a kotu
  • Masu yada bidiyoyin sun yi ikirarin cewa kotun sauraron kararrakin zabe ta soke nasarar da Tinubu ya samu ta zama shugaban kasa
  • Sai dai wani bincike gaskiya da gaskiya da aka gudanar ya nuna cewa har yanzu kotun ba ta yanke hukunci ba, kuma murabus din Adamu ba ya da alaka da hakan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wani faifan bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta na Facebook, ya yi iƙirarin cewa Abdullahi Adamu da ya ajiye mukaminsa na shugaban jam'iyyar APC, yana da alaƙa da shari'ar zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A cewar faifan bidiyon, wanda ya fara bayyana a yanar gizo a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, 2023, Adamu ya sauka daga muƙaminsa ne bayan gano cewa kotun zaɓe ta soke nasarar Shugaba Bola Tinubu kan ya kasa samun kaso 25% na ƙuri'un da aka kaɗa a Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Ba saboda Tinubu Adamu ya ajiye mukaminsa ba
Ba saboda shari'ar zaɓen Tinubu Abdullahi Adamu ya yi murabus ba. Hoto: Olukayode Jaiyeola/Nur, Kola Sulaimon/AFP
Asali: Getty Images

Ba gaskiya ba ne, murabus din shugaban jam'iyyar APC ba ya da alaƙa da zaman kotun da ake yi

Da yake magana a cikin yaren Pidgin, wani mutum ya ce Adamu ya sauka ne domin nesanta kansa daga abubuwan da ya ce Tinubu na yi da suka hada da tsoratar da alƙalai da ba su cin hanci saboda suna shirin soke zaɓensa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai rahoton The Cable ya nuna cewa Adamu ya ajiye muƙaminsa na shugabancin APC ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli, saboda al’amuran jam’iyyar.

An wallafa wani bidiyon da ya alaƙanta murabus ɗin Adamu da zaman kotun zaɓe

An kara wallafa wani bidiyon na daban da ya yi irin wannan ikirarin na cewa Adamu ya yi murabus ne saboda shari'ar zaben shugaban kasa da ake yi.

Kara karanta wannan

“Bata Lokaci Da Yaudara Ne Kawai”: Atiku Ya Caccaki Jawabin Shugaba Bola Tinubu

Bidiyon da aka yi da yaren Pidgin, an fassara shi zuwa:

“Daga karshe, kotu ta gama shiryawa tsaf don tsige Tinubu. Shugaban APC ma ya yi murabus cikin gaggawa.”

Bidiyoyin sun sake bayyana a cikin wasu saƙonni na Facebook da suma suka yi irin wancan iƙirarin a nan, da kuma nan.

Binciken gaskiya ya tabbatar da cewa ba bu maganar soke zaɓen Tinubu

Sai dai wani shafi na binciken gaskiya mai suna Africa Check, ya duba don ganin ko da gaske ne kotun zabe ta soke nasarar Tinubu, wanda dalilin haka ake zargin Adamu yayi murabus.

Bayan gudanar da bincike, Africa Check ta gano cewa, ba gaskiya ba ne maganar soke nasarar Tinubu.

Abu na biyu kuma, babu wata shaida da ke tabbatar da iƙirarin cewa murabus ɗin Adamu na da alaƙa da abubuwan da ke faruwa a kotun zabe.

An gabatar da sahun ƙarshe na ministocin Tinubu

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa

Legit.ng ta kawo muku rahoto kan sahu na ƙarshe na mutanen da Shugaba Tinubu zai naɗa ministoci.

A cikin sunayen akwai tsofaffin gwamnoni aƙalla guda 5 da kuma sauran maƙarraban jam'iyyar APC da suka daɗe suna hidimar ma ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel