Gwamnan APC Ya Jawo Yaron Tsohon Gwamna, Ya Samu Babbar Kujera a Rabon Mukami

Gwamnan APC Ya Jawo Yaron Tsohon Gwamna, Ya Samu Babbar Kujera a Rabon Mukami

  • Gwamnan jihar Katsina ya amince da nadin wasu mukamai na shugabannin hukumomi a gwamnati
  • Mallam Dikko Umaru Radda, PhD ya sanar da karin masu bada shawara da taimakawa na musamman
  • Yaron tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya shiga cikin mukarraban sabon Gwamnan jihar

Katsina - A kokarinsa na ganin ya jawo wadanda za su taimaka masa wajen gudanar da aiki, Gwamnan jihar Katsina ya nada karin sababbin hadimai.

Tun daga masu bada shawara, Gwamna Dikko Umaru Radda, ya sanar da cewa ya amince da nain masu bada shawara da shugabannin hukumomi.

Babban Mai taimakawa Gwamnan a kafofin sadarwa na zamani, Malam Isah Miqdad Jr. ya fitar da sanarwar a yammacin ranar Litinin a shafin Twitter.

Gwamna
Gwamnan Katsina, Umaru Dikko Radda PhD Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Har da 'dan Aminu Bello Masari

Legit.ng Hausa ta lura a cikin wadanda aka ba mukaman har da yaron Aminu Bello Masari wanda shi ya yi Gwamna a jihar Katsina tsakanin 2015 da 2023.

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1 Alhaji Abdulkarim Aminu Bello Masari - Mai bada shawara a kan harkoki na musamman.

1- Injiniya Yakubu Nuhu Danja - Mai bada shawara a kan tattalin arzikin karkara

2- Hajiya Hadiza Maikudi - Mai bada shawara a kan harkokin gwamnati

3- Hajiya Jamila Abdu Mani - Mai bada shawara a kan ilmin ‘yan mata.

4- Alhaji Sabo Musa Hassan – Babban Mai bada shawara a kan harkar addini

5- Arc. Bashir Mohammed Idris – Mai taimakawa a kan sha’anin gidaje.

6- Alhaji Muhammad Lawal Zubairu – Mai kula da cibiyar sana'ar matasa.

7- Alhaji Umar Sabi'u Sukuntuni- Magatakardar cibiyar sana'ar matasa.

8- Alhaji Shamsudeen Sanusi Ahmed – Darekta Janar na tsarin aiki.

9- Mallam Nurudeen Mohammed Tela- Mai taimakawa Gwamna a kan harkokin baitul-mali.

Gwamnan jihar Katsina ya ce wadanda aka zaba za su fara aiki ne ba tare da wani bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Tausayin talaka: Zulum da wasu gwamnoni 2 sun kawo hanyar rage radadin cire tallafi

Tinubu za su tafi Cotonou

An samu rahoto Dele Alake ya shaida cewa an gayyaci Bola Ahmed Tinubu zuwa bikin taya Benin cika shekara 63 da samun ‘yancin kai a tarihi.

Gwamnonin Jihohin Ogun, Legas, Oyo, da Neja; Dapo Abiodun, Babajide Sanwo-Olu, Seyi Makinde da Umar Bago da wasunsu su na cikin ‘yan rakiyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel