'Ba Batun Neman Ministan Bayelsa Ya Kai Ni Wajen Tinubu Ba', Jonathan Ya Yi Bayani
- Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya musanta raɗe-raɗin da ake yi kan ziyarar da ya kai wa Shugaba Tinubu
- Ya ce ba batun neman ministan jihar Bayelsa ne ba ya kai shi fadar shugaban ƙasa
- Ya bayyana cewa wasu masu neman tada zaune tsaye ne ke yaɗa labaran ƙarya a kansa
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya musanta zargin da ake masa na cewa yana ƙoƙarin sanya baki kan ministan da Tinubu zai zaɓo daga jihar Bayelsa.
Jonathan ya bayyana hakan ne a martanin da ya mayarwa wata ƙungiyar dattawan jam'iyyar APC ta jihar Bayelsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An zargi Jonathan da saka baki wajen zaɓen ministan jihar Bayelsa
Dattawan na APC a jihar Bayelsa sun koka kan cewa tsohon shugaban ƙasar na yunƙurin tsoma baki kan wanda za a naɗa minista daga jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai Jonathan a martanin da ya mayarwa ƙungiyar, ya ce akwai yiwuwar wasu daga cikin 'yan siyasar jihar ta Bayelsa sun yi wa ziyarar da ya kai wa Tinubu mummunar fassara.
Mai taimaka ma sa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mista Ikechukwu Eze, ya bayyana cewa Jonathan ya ziyarci Tinubu ne don tattauna batutuwan da suka shafi ECOWAS da yake shugabanta ba wai batun neman minista ba.
Jonathan ya nemi 'yan Najeriya da su yi watsi da jita-jitar
Eze ya kuma nemi 'yan Najeriya su yi watsi da jita-jitar da ya ce ba ta da tushe balantana makama, wacce ta fito daga wasu mutane da ke neman tayar da zaune tsaye kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce jam'iyya mai mulki ba ma ta san da zaman mutanen da ke kiran kansu da dattawan jam'iyyar APC na jihar Bayelsa ba.
Ya ƙara da cewa wasu gungun mutane ne da suka rasa madafa, shi ne suke ƙoƙarin ƙirƙiro irin waɗannan labarai na ƙarya domin cimma wata mummunar manufarsu a kan Jonathan.
Eze ya kuma bayyana cewa tuntuni mutanen ke son ganin Jonathan ya wulaƙanta, amma kullum akasarin hakan suke gani, tunda ga shi kullum sai ƙara samun ci gaba yake yi.
An bayyana ranar da sunayen ministocin Tinubu za su isa Majalisar Dattawa
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan ranar da aka bayyana cewa sunayen ministocin Tinubu za su isa Majalisar Dattawa.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa Tinubu ya shaida masa cewa sunayen za su iso majalisar ranar Alhamis mai zuwa.
Asali: Legit.ng