Dattawan APC na Fada da Tsohon Shugaba Jonathan kan Nadin Ministocin Tinubu

Dattawan APC na Fada da Tsohon Shugaba Jonathan kan Nadin Ministocin Tinubu

  • Kungiyar dattawan APC a Bayelsa ta ce Dr. Goodluck Jonathan ya dage sai an ba shi kujerar Minista
  • Michael Adomokeme ya zargi tsohon Shugaban Najeriyan da neman girban abin da bai shuka a zabe ba
  • Bayelsa ta na da kujera akalla daya a FEC, ‘Yan APC sun ce Jonatan yana so ya kawo wanda za a nada

Bayelsa - Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Bayelsa, sun tashi tsaye a game da abin da su ka kira “yunkurin” Goodluck Jonathan.

Daily Trust ta ce ‘yan siyasar su na zargin tsohon shugaban na Najeriya da kokarin kai wa Bola Ahmed Tinubu sunan wanda zai ba Ministansu.

Bayelsa kamar kowace jihar kasar nan, ta na da kujera daya a majalisar FEC, a cewar ‘ya ‘yan na APC, Goodluck Jonathan yana harin kujerar nan.

Kara karanta wannan

"Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jawowa Abdullahi Adamu Rasa Shugabacin APC"

Tinubu da Jonathan
Bola Tinubu da Goodluck Jonathan Hoto: @fkeyamo
Asali: Twitter

Ba ayi kaso da Jonathan a APC ba

Dattawan da su ka fito a karkashin kungiyar Bayelsa APC Elders Council sun zargi tsohon shugaban da neman ganima bayan bai je yaki ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar ‘yan siyasar, Dr. Jonathan ya tallata Atiku Abubakar ne a zaben shugaban kasa da aka yi, su ka ce bai goyo bayan APC da Bola Tinubu ba.

Shugaban kungiyar, Cif Michael Adomokeme ya yi magana da manema labarai a Yenagoa, ya ce bai dace Jonathan ya girbi abin da bai shuka ba.

Halin da ake ciki tamkar mutum ya yi wa kamfani aiki ne, Michael Adomokeme yake cewa sai ya je neman albashi a wani kamfanin na dabam.

Adomokeme : "Tinubu ba zai yi mana haka ba"

Punch ta rahoto ‘dan siyasar yana mai cewa Bola Tinubu kwararren ‘dan siyasa ne wanda ya san darajar sakawa wadanda su ka taimaka masa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

Kungiyar dattawan na sa ran Tinubu ba zai bari kura ta ci bugu, gardi ya karbi kudi ba.

Tun da aka kafa APC mai-ci a yau, Adomekeme ya ce su ka shiga jam’iyyar, a cewarsa a wancan lokaci tamkar abin kunya ne rajista da su a Bayelsa.

“Ya yi shugaban kasa na shekaru shida, ya nada tulin Ministoci. Meyasa yanzu ya damu da kujera daya da jam’iyyar APC ta ke son samu a Bayelsa?
Shin yana kokarin hana APC samun nasara ne a zaben Nuwamba? Ba a saba ji ba, abin kunya ne tsohon shugaban kasa ya je neman kujerar Minista.”

- Michael Adomokeme

Ana canza lissafi a Aso Rock?

Ana da labari cewa har yanzu dai Sanatoci su na sauraron Shugaban kasa, kwanaki kadan su ka ragewa Bola Tinubu ya fito da sunayen Ministocinsa.

Har yanzu sunayen wadanda za su iya zama Ministoci bai bar Aso Rock ba, ana tunanin cewa ana ta ‘yan canje-canje da askin ya zo gaban goshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel