C3GR Ta Gargadi Tinubu Kan Ba Ganduje, Doguwa Mukamai, Ta Bayyana Dalili

C3GR Ta Gargadi Tinubu Kan Ba Ganduje, Doguwa Mukamai, Ta Bayyana Dalili

  • Wata kungiya a Najeriya ta yi gargadi kan shirin ba wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje mukamai kan zargin badakala
  • Kungiyar ta kuma gargadi kakakin majalisar kan ba wa Honarabul Alhassan Doguwa mukami saboda zargin kisan kai
  • Kungiyar ta bayyana haka a cikin wata takarda da ta tura wa Shugaba Tinubu da kakakin majalisar, Abbas Tajudden

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Gamayyar Rajin Tabbatar da Kyakkyawan Shugabanci (C3GR) ta koka kan wasu nade-nade da Shugaba Tinubu ke shirin yi.

Shugaban kungiyar, Adebowale Rasheed shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya turawa Shugaba Tinubu da kakakin majalisa, Abbas Tajudden.

Kungiya Ta Gargadi Tinubu Kan Ba Wa Ganduje, Doguwa Mukamai
Kungiyar C3GR Ta Ja Kunnen Tinubu Kan Ba Wa Ganduje Mukami Duba Da Zargin Da Ke Kansa. Hoto: Vanguard.
Asali: Facebook

A cikin takardar da ta aike, kungiyar ta ce a halin yanzu bai kamata a ba wa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Alhassan Doguwa mukamai ba saboda korafe-korafen da ke kansu, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu: COEASU Ta Umarci Mambobinta Su Na Zuwa Aiki Na Kwanaki 2 Kadai A Sati Bayan Cire Tallafi

Kungiyar ta gargadi Tinubu kan Ganduje da Doguwa

Ya ce a doka Ganduje ya cancanci a ba shi mukami amma kuma bai dace ba duba da irin badakalar da ake zarginshi da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce ganin yadda aka gano tsohon gwamnan a cikin wani faifan bidiyo ya na dura daloli a aljihunsa, hakan na nuna alamun shakku akansa.

A cewar sanarwar:

"Mai girma shugaban kasa, kasan cewa wannan ba lokacin da ya dace ba ne a ba wa wani da ake da shakku akansa mukami.
"Wanda a ko wane lokaci za a iya gayyatar shi don amsa tambayoyi akan hakan.

Ta bayyana irin korafe-korafen da ke kansu

Ya kara da cewa ba wa Ganduje wani mukami zai iya bata sunan gwamnatin nan da ake ganin ta fara da kafar dama, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

A takardar da kungiyar ta tura wa kakakin majalisar, ta koka kan shirin ba wa Alhassan Doguwa mukamin shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri.

Ta bayyana yadda ake zargin Doguwa da kisan wasu mutane da dama yayin babban zabe da aka gudanar.

Kungiyar ta kirayi Abbas Tajudden da kada ya kuskura ya jawo wa majalisar abin kunya wurin ba wa Doguwa mukami.

Kotu Ta Dakatar Da Gayyatar Da Aka Yi Wa Ganduje Kan Bidiyon Dala

A wani labarin, Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci kan gayyatar tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje.

Hukumar yaki da cin hanci a jihar Kano na binciken Ganduje kan badakalar bidiyon dala da ake yadawa a lokacin mulkinsa.

Hukumar ta gayyaci Abdullahi Ganduje a ranar 6 ga watan Yuli don amsa wasu tambayoyi a ofishinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel